Mallakar Bita Zaizai

MAGANIN MALLAKAR BITA ZAI ZAI 

Assalamu alaikum jama'a ƴan uwa maza da mata masoya Annabi Muhammad SAW, mabiya wannan shafin namu mai albarka na Shehudiezer, barkan ku da wannan lokaci da fatan kun wuni cikin qoshin lafiya, Ubangiji Allah ya sa haka amin. Ni Shehu diezer ina gaishe ku ina yi muku fatan alkhairi duniya da lahira Alfarmar Alqur'ani.

A Yau kuma na zo muku da wani gagaruman sirruka guda 2 na maganin mata ko ince BITA ZAIZAI na cikin gida wanda zakayi /zakiyi da kan ki ki mallake mijin ki /saurayin ki /budurwar ka/ matar ka cikin sauqi, na kawo wannan sirrin ne a online saboda qorafe qorafe da yawan tambaya da kuma nuna buqatuwar wannan sirri da jama'a suke yi.

Da farko dai shi wannan maganin mata yanda ake haɗashi shine ana so aje kasuwa wurin masu siyarda itace da ganyen maganin gargajiya kace a baka BITA ZAIZAI, idan ka siyo iccen Bita Zaizai sai ka ebo gero a hannunka haka daidai wanda zai iya shigewa bakin ka, ba mai yawa sosai baka, in ka ebo sai ka haɗa shi da bita zai zai ɗinnan ka zuba su a bakin ka kayi qoqari barci ya ɗaukeka, idan kayi barci ka tashi wannan geron da bita zaizai ɗin yana cikin bakin ka sai ka fito da su ka daka su su daku, saj ka dinga sakamata a abinci tana ci, in ma budurwar ka ce zaka iya dinga siyamata abun ci ko awara ko dankali ko nama ko tsire da sauran su sai ka dinga barbaɗa mata a ciki, sannan kuma a dai dai ranar da za'a fara saka mata maganin a abinci ana so ka dinga rubutawa kokuma kasa a dinga rubuta maka "mãliki yaumiddin" qafa bakwai (7) amma za'a buɗe minjayen (mimun) ta farko ta “Mãliki” kamar haka yanda zaku gani a cikin wannan photon. 👇Bayan an yi rubutun kuma an buɗe mimun ɗin sai a rubuta sunan wanda ake so a mallake a cikin mimun ɗin a wanke duka a shanye, ayi haka kamar sau uki (3) ko sau bakwai (7), in dai an yi hska to aiki ya kammala, mujarrabun, za'a ga abun mamaki da ikon Allah. 

Wlh na san sai kun neme ni kun yi mun godiya, Allah ya qarawa Annabi daraja.

Wannan sirrin sirrine mai tasiri sosai, wallahi maganin mata ne mai kyau, wannan shine natural bita zaizai ainihin sa, amma aji tsoron Allah.

Allah yasa a dace.

Domin neman qarin bayani kokuma domin waɗanda suke so a yi musu wani aiki su tuntuɓeni a wannan numbobin nawa, 08136560680, 09020132884, in ba'a same mu a 1 ba a kira ɗayar za'a same mu, Mun gode, Allah ya sa mu dace.

ASIRIN BITA ZAIZAI 2

Assalamu alaikum, da fatan kuma biye da ni, wannan sirrin na biyu shima sirri ne mai qarfi daga Malam Namadi Muhammad Gagare, wannan aikin ana yin sa ne Ranar lahadi ake yin sa.

Za'a samu ko a nemo ko a siyo Tawwadar Jan Miski da Za'afarãn na ruwa, wannan tawadar ana siyar da ita a gurin siyarda tiraruka da Qur'anai da littattafan qananunnuka da sirruka da kayan rubuce rubucen larabci, in an samo ta ko an siyo ta ko an haɗa ta sai a rubuta waɗannan ayoyin👉 “ZUYYINA LINNÃSI HUBBUSH SHAHAWÃTI MINANNISÃ'I WAL BANEENA WAL QANÃƊEERIL MUQANƊARATI MINAZZAHABI WAL FIDDATI WAL KHAILIL MUSAWWAMATI WAL AN'ÃMI WAL HARS, ZÃLIKA MATÃ'UL HAYÃTIDDUNYÃ WALLAHU INDAHU HUSNUL MA'ÃB” qafa ɗaya (1)

“WALAQAD HAMMAT BIHI WAHAMMA BIHA” qafa ɗaya (1)

“WA ALQAITU ALAIKA MAHABBATAN MINNI” qafa ɗaya (1)

Sai kuma wannan hatimi wanda zan rubuta a qasa shima za'a rubuta shi qafa ɗaya (1) a haɗa da waɗancan ayoyin na sama a wanke da Ma'ul Wardi (rose water) asha, ga hatimin👇Nasan wasu zasu tambaya menene Ma'ul Wardi, to Ma'ul Wardi shine ruwan fure🌹, wani ruwa ne mai kyau ana siyar da shi a shagunan magungunan gargajiya, akwai qaramar kwalba akwai babba, ga hoton babbar kwalbar Ma'ul Wardi 👇Bayan an rubuta duka ayoyin da hatimin an wanke da ruwan Ma'ul Wardi ɗin an sha shikenan an gama wannan ɓangaren, sai kuma a sake rubutawa, iri ɗaya the same za'a rubuta kamar yadda aka yi aka sha, in an sake rubuta wani sai a wanke da ruwa ɗan kaɗan, sai a samu Furen duman rafi (in an je wurin masu siyar da itatuwa da magungunan gargajiya za'a sameshi), in an samo shi a daka shi sama sama ba sosai ba, sai a zuba a cikin rubutun ɗan kaɗan ɗin.

Bayan an yi haka sai a siyo farin kwalli wanda ba dakakke ba Dutsi ɗaya (1) babu tayi, ma'ana in kaje siya bazaku yi ciniki da mai siyarwar ba, misali in kace “abaka kwalli” aka ɗauko maka shi kace nawa ne aka ce ɗari biyar, to kawai ka cire ɗari biyar ɗin ka bayar, kar kace a yi maka ragi kokuma kace nawa ne sauqin sa, ba'a tayawa, bayan ka siyo Dutsin kwallin ka dawo gida sai ka saka shi a cikin rubutunnan da ka wanke ɗan kaɗan wanda ka sakawa Furen duman rafi, in ka saka Dutsin a ciki sai ka barshi ka samu wuri mai kyau ka ajiye rubutun ka rufe shi, ba zaka qara bude shi ba ko aiki da shi sai sati ya zagayo Ranar wata Lahadi kenan, in Lahadi ta zagayo sai ka cire Kwallin ka fasa shi, idan zakaje wurin yarinyar sai ka ambaci sunan ta da Bismillah sai kashafa kaje, in kuma mace ce idan zaki fita fira wurin saurayinki in yazo kokuma idan kinsan in kin fita zaki ganshi ko zaku haɗu sai kiyi Bismillah ki kira sunansa ki shafa kitafi, misali ida mace ce misali in Maryam ne sunanta, ka shirya zaka je wurin fira sai kace “Bismillahi, Maryam” sai ka shafa ka tafi wurinta direct, in namiji ne misali “Bismillahi, Qasimu”, sai ki shafa, a dinga yin haka kamar sau 3 in aka yi ko sau 7 to magana ta qare.

Tabɗijam, duk wanda ya shiga komar wannan aikin wallahi sai ta Allah, ahi tsoron Allah jama'a, a kula wurin yin wannan aikin, kar a ci hakkin wani ko wata, kar a yaudari wata ko wani, kar ayi da niyyar wulaqanta wata ko wani. Akwai mutuwa kuma akwai hisabi akwai tambayoyin qabari akwai kwanciyar kabari. Allah ya sa mu dace amin.

Duk wanda yake da tambaya ko neman qarin bayani game da wannan sirrin ko wani sirri wanda na yi posting a wannan website ɗin nawa ko yake so a yimasa wannan aiki sai yayi comment kokuma ya kirani a waya ya tambayeni 08136560680

Muna yin aiki ko wane irin aiki, in dai na magunguna ne da na asrarai da na addu'o'i da na shawarwari ne, duk wanda yake da wata irin buqata game da matsalar aure ko matsalar alaqa ko soyayya ko firaqu ko kasuwanci ko takarar mulki ko ɗan siyasa ko dafa'i ko jalabi ko istihara ko Ramli da binciken rayuwa da istihara da binciken aure da gane yanda aure zai kasance yanda halayen amaren yake, duk ina yi, idan ka gayamun sunanka da sunan mahaifiyarka to ba tare da na sanka ba ma ba tare da ka yimun bayanin komai ba zan gaya maka halayen ka da kamanninka da komai naka da irin abubuwan da kake so da irin abubuwan da baka so, da dabi'uka da matsalolinka duka.


Domin neman qarin bayani ko yake son wani aiki ko bincike sai ya kirani a numbobin wayata gasu kamar haka:

08136560680 Call and WhatsApp

09020132884 Call
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url