Sirrin Mallakar Mijin Aure Ko Matar Aure

SIRRIN MALLAKAR MIJIN AURE KO MATAR KA TA AURE

 Assalamu alaikum warahmatullah ta'ala wabarakaatuh ƴan uwa mazan aure da matan aure wannan sirruka guda biyu da zan bayar na yau naku ne, wanda bashida aure ko wacce bata da aure dan girman Allah kada ya kuskura ko kada ta kuskura ta yi wannan ayyuka musamman wannan na farkon, haramun ne ga wadanda basa da aure su yi wannan aikin, domin kwata kwata ba layin su bane wallahi, wannan aikin na samar da shi ne saboda yanda ake samun matsala a zamantakewar aure da mu'amalar yau da gobe a tsakanin ma'aurata, da faɗa da rashin ganin darajar juna, da rashin zaman lafiya da rashin kwanciyar hankali da fahimtar juna, da saurin fushi, to ga aikin da zaki yi cikin sauqi ki mallake zuciyar mijinki kokuma hankalin sa, kaima ga aikin da zaka yi domin mallake zuciyar matar ka a cikin sauqi, a yi qoqari a gwada saboda a rage samun matsalolin da suke kaiwa ga rabuwa a tsakanin ma'aurata da saurin yaji da saurin yanke hukunci a cikin furuci, wannan mallaka ce fa mai qarfi yanda bakwa tinani, Insha Allah zata yi aiki sosai.

Da farko dai za'a qudurta kyakkyawar niyya, ayi domin Allah, ba domin wata manufa ba, ba domin samun wani abu na duniya ba, kokuma wata muguwar ma'ana ta cutarwa, sannan kuma wannan sirrin na matan aure da mazajen aure ne kawai kamar yanda na fada tin a farko, ana yin wannan aikin zuwa kwana uku 3, aiki ne na kwana uku kullum za'a yi har zuwa kwana uku, a rubuta wannan ayoyin “Fadamdama alaihim” kamar yanda kuke gani a qasa a cikin wnanan hoton👇Amma ana yin rubutun ne wake wake, ma'ana Fadamdama alaihim ɗin qafa ɗaya 1 da wasali za'a rubuta, qafa ɗaya kuma babu wasali za'a rubuta, qafa ɗaya kuma babu wasali kuma ba ƴaƴa ma'ana ba'a ɗigo akan haruffan, amma za'a buɗe mimun ɗin duka sannan a saka suna, in miji ne zai mallake matar sa sai ya saka sunan ta, in kuma mata ce zata yiwa mijinta sai ta saka sunan sa a cikin mimun mimun ɗin da aka buɗe, bayan an rubuta sai a wanke rubutun da ruwa ƴan kaɗan bada yawa ba, ƴan kaɗan sosai, sai a samu tirare mai qamshi na ruwa mai maiqo sai a haɗashi da wannan rubutun, a lokacinda zaka sadu da matar taka/ kika san zaki sadu da mijinki sai kiyi tsalki ko kayi tsarki da wannan haɗin tiraren da rubutun, ana yin haka kullum harzuwa kwana 3, to wlh Mallaka ce ta yankan shakku take yanke zaki ga chanji, ba zai qara neman wata mace fiye da ke ba, in ma kina da kishiya to daga ranar kin fita kima da daraja da ɗanɗano a wurin sa Insha Allah.

Mujarrabi ne

SIRRIN MALLAKAR MIJI KO MATA 2

Assalamu alaikum mabiya shafina, shi wannan aikin ana buqatar a samu ganyen gamji guda bakwai (7) banda wanda yafaɗo qasa, ma'ana in ma zuwa aka yi ebowa a jikin bishiyar to ba'a ɗaukar wanda ya fãɗi a qasa, saidai a hau kan bishiyar kokuma a tsinko ganyen daga kan bishiyar ganye guda bakwai (7), kowanne daga cikin ganyayyakin a rubuta masa Fatiha qafa ɗaya (1) amma kowacce Mimun da Ha'un na cikin rubutun za'a buɗe su za'a saka sunan wanda ake so a mallake a ciki, sai a shanya su ko a cikin daki ko a fili su bushe, idan suka bushe qamas sai a haɗa da ganyen gogamasi da kitsen farar kaza idan mace za'a mallake a daka su sosai, idan namiji ne za'a mallake to kitsen farin zakara za'a nemo sai a haɗa da ganyen goga masi ɗin da ganyen gamjin da ya bushe, idan aka daka su suka daku sai a dinga tirara golaye ko ince gwalake (testicles), haka itama idan mace ce sai ta dinga tirara gabanta da shi, ana so a dinga faɗar buqata a daidai lokacin da ake yin tiraren

Qarin bayani gameda time ɗin da ya kamata a dinga yin Tiraren, amma ba dole bane kuma ba tilas bane, kuma rashin yin tiraren a cikin waɗannan lokutan da muka ambata ba zai hana aikin tasiri ba, amma idan aka yi a cikin lokutan to added advantage ne, zai qara qarfi sosai👇

Idan kai namiji ne idan zaka yi tiraren sai ka dinga yi a lokacin venus (zuhra)
Ke kuma idan mace ce ki dinga yi lokacin tauraron sun (shams) ko moon (qamar), domin sanin yaushe ne taurarin shams ko zuhra ko qamar sune sharafi sai ku yi download ɗin application mai suna Chogadia Hisab, ga hoton yanda application ɗin yake 👇

       Haka hoton application ɗin yake 👆


Cikin application ɗin kuma haka yake👇Idan kun kura a hoto na biyu da na turo wanda yake nuna yanda cikin application ɗin yake zaku ga sunan taurari dayawa, a cikinsu zaku ga taurarin da muke bayani a kan su, kamar shamsu in kun duba gefen hagun sa zaku ga an nuna cewa tauraron zai fara sharafi qarfe 7:08am-8:12am, sai kuma taurarin Qamar shima zaku ga application ɗin ya nuna cewa zai fara sharafi qarfe 10:21am-11:26am, sai na qarshe wanda ya nuna zai fara sharafi qarfe 3:43pm-4:48pm, to a haka suke a kullum suna chanza lokaci, kowane tauraro yana da lokacin da yake sharafi a duniya, kuma kowanne tauraro yana da amfani da kuma irin addu'a ko aikin da ake yi a lokacinda yake sharafi, kuma kullum canzawa lokacinsu yake yi.

 Bayan haka kuma idan kin san mijinki driver ne ko tana aiki a wani gari yana jimawa bai dawo ba to kar ma kiyi wannan aikin bazai yi aiki ba haka kaima idan matar ka nurse ce ko tana yawo ko tana zuwa gurin aiki ta kwana a chan, kokuma ba a gari ɗaya kuke ba to aikin ba zai yiba ko kayi shi in dai bakwa kusa, saboda dole idan ana yin hayaqin yazama ana saduwa akai akai


Domin neman qarin bayani kokuma wanda yake da tambaya ko neman qarin haske sai a yi comment da tambayar kokuma masu so a yimusu wani aiki irin wannan ko aiki game da wata matsalar su zasu iya kirana a numbobina👇
08136560680 (WhatApp and Call), 09020132884 Kira
Ga link na WhatsApp group dinmu:


E-mail:


YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa

Alhamdulillah
Next Post Previous Post
2 Comments
 • DR.ALH NASIR BUNUNU
  DR.ALH NASIR BUNUNU February 15, 2022 at 2:00 AM

  Allah saka da alkhairi

  • Shehudiezer
   Shehudiezer July 1, 2022 at 8:29 AM

   Ameen ameen

Add Comment
comment url