Sirrin Mallaka Na Yankan Shakku

SIRRIN MALLAKAR MACE KO NAMIJI (kar ka kuskura kayi idan kasan ba auren yarinya zaka yiba)


 Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakãtuhu jama'a al'ummar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, ina gaishe ku tare da fatan alkhairi a gareku da nisan kwana mai albarka, Allah ya qara mana lafiya da zaman lafiya, yabamu kwanciyar hankali da masoya na gari, Allah ya haɗamu da fuskar manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama amin amin.

Kamar kullum dai yau ranar Litinin albarkacin ita ce ranarda aka haifi manzon tsira Annabi Muhammad SAW na zo muku da babban sirri na ayoyin mallaka da sirrin mallake mutum, namiji ko mace.

Bayan haka wannan sirri da zan bayar a gaskiya ban so in bayar dashi ba wallahi, saboda illolin wannan zamani dakuma ruɗin zuciya da rashin tsoron Allah, saboda gudun kar a yaudari wata/ wani, a mayar dashi kamar bawa kuma ba tare da auren sa zaki yiba kokuma ba auren ta zaka yiba, amma dai ya zama dole in sakeshi saboda irin yanda mabiyana suke complain akan cewa ya kamata a qara musu sirri mai yankan wuqa mai yankan shakku akan mallaka da janye hankalin wanda ake so shi ya sa zan bayar dashi, saboda haka a kula sosai, dan Allah aji tsoron Allah bayin Allah ƴan uwa, wannan ba sirrin fatiha na mallaka bane, sirrin fatiha na mallaka zan sakeshi anan gaba Insha Allahu 

 Ba tare da ɓata lokai ba ga yanda kaifiyyar aikin take👇

Da farko dai za'a je kasuwa wurin masu siyarda ganyen itatuwa da garin itatuwa na gargajiya kokuma maganin gargajiya kokuma wurin masu Islamic Chemist kokuma wurin masu siyar da littattafai da qur'anai na warsh a siyo gããrin ganyen Hatiful qalbi, Insha Allah za'a sameshi a cikin irin waɗannan shaguna da na ambata muku, a tambaya sosai, kuma ana siyar da shi Naira 200 zuwa ɗari 300, ko 500 in yayi tsada, ga misalin hoton yadda gããrin hatiful qalbi ɗin yake👇👇          Wannan👆 shine HATIFUL QALBI  


Bayan an samo garin icen Hatiful Qalbi ɗin Sannan a samu allo na rubutu kokuma ka samu wanda zai rubutamaka abunda ake so a rubuta, ko wani almajirii ko wani malami wanda zai iya dinga rubutamaka wannan rubutun kokuma wanda zai rubutamaka na tsawon kwanakinda ake so yabaka ka ajiye.

In ka samu allon kokuma wanda zai dinga rubuta maka, sai a rubuta wannan ayar👇

"وأَلَّفَ بين قُلُوبِهِمْ لَوْ أَنفَقْتَ ما في الأرض جَمِيعًا مَا أَلَّفْتَ بَيْنَ قُلُوبِهِمْ ولكن الله أَلَّفَ بَيْنَهم إِنَّهُ عزيز حكيم"

“Wa allafa baina quluubihim lau anfaqta mã fil ardi jamee'an mã allafta baina qulubihim walakinnal laha allafa bainahum innahuu azeezun hakeem” Qafa arba'in da ɗaya (41)

 Amma kuma duk mimun za'a buɗe abar gurin saka suna, za'a rubuta sunan wanda yake so ya mallake wani a sama sai sunan wanda ake so a mallake a qasa, kamar haka yanda kuke gani anan wani rubutun ne da nayiwa wani bawan Allah👇👇👇In an gama rubutun za'a dinga zuba wannan garin hatiful qalbi ɗin a motsa ana sha da asuba kafin rana tafito kokuma kafin aci komai, ma'ana zakayi rubutun tin da rana kenan kokuma kafin kakwanta ka tabbatar kaa gama rubutun ayar qafa arba'in da ɗaya (41) kaa wanke ka ajiye, shi kuma wannan garin maganin na Hatiful Qalbi ɗin zaka kwatanta yadda zaka dinga barbaɗa garin hatiful qalbi ɗin a cikin rubutun ta yanda zai kai sati ɗaya daidai kana sakashi a rubutun bai qareba.

To wallahi in dai an yi rubutun daidai kuma kasha kullum ka yi dai dai to kafin kagama aikin rubutun zaka fara ganin chanji taɓangaren kallo kokuma yawan damuwa da kai kokuma wani chanji dai wanda baka saba ganinsa daga gurin wanda kake son ba, haqiqa nasha mamaki wallahi a lokacinda nayi wannan aikin, ina taqama da wannan aikin yana daga cikin manya manyan asirai na mallaka da na yarda da ingancin su da ijabar su, kuma wlh ko bakwayin magana zakaga ikon Allah in kayi wannan aikin Insha Allah matuqar kuna ganin juna kokuma kuna magana da juna, zaka ga yanda zata nunamaka qiri qiri tana sonka kokuma yanda zai nuna maki qiri qiri yana sonki.
Na rantse da girman Allah ni da kaina na gwada wannan sirrin, kuma shine sirrin da na fara yi a rayuwata na mallaka, kuma yayi mun aiki kafin in gama yin sa ma naga chanji, kuma dana gama aikin tin 2017 har yau soyayyar tananan wallahi bata yankeba, in taqaicemuku har munyi aure a wannan shekarar ta 2023, kuma muna zaune lami lafiya alhamdulillah.
Akula sosai: wurin rubuta sunan a cikin mimun ɗin zaka rubuta sunan ka a sama sannan sunan yarinyar a qasa, kokuma sunan wanda ake so kokuma sunan wanda ake so a mallake shi kaɗai acikin mimun ɗin , in mace ce zaki iya rubuta sunan mutumin shi kaɗai kokuma ki rubuta sunan ki a sama sunan mutumin a qasa, kuma qafa 41 za'a dinga rubutawa kullun ana saka garin Hatiful Qalbi ana sha tsawon kwana 7.


A jarraba kuma ayi sharing a turawa ƴan uwa kokuma kayi copy zuwa abokanan ka waɗanda suke da irin wannan matsalar wannan link ɗin https://www.shehudiezer.com sushigo sukalli maganin matsalarsu, dama wasu magunguna da sirruka da laqani kala kala a cikin wannan shafin nawa.
Sannan kuma mutane waɗanda suka karanta ba zasu iya yiba suke so muyi musu wannan aikin kokuma wani aiki na sirri kokuma wani aiki daban za su iya yimun magana a WhatsApp ko sukiramu a wannan numbar tamu 08136560680, ko 09020132884 kokuma su yimana magana ta WhatsApp da numbar 08136560680, za'a samemi.

Alhamdulilllah

Masu tambaya zasu iya yin tambayarsu a comment kokuma su kirani a waya su tambayeni kokuma sumun magana a WhatsApp.

Subhana rabbika rabbil izzati amma yasifuun, wasalamun alal mursaliin, walhamdu lillahi rabbil alameen.

Ina da shafin Instagram da facebook da twitter da YouTube, duka zaku iya following dina ga links👇

Bayan haka ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
Tiktok: 
YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa

Alhamdulillah 

Next Post Previous Post
1 Comments
  • Unknown
    Unknown August 23, 2021 at 8:04 AM

    Mashallah

Add Comment
comment url