Maganin Typhoid Cikin Sauqi

MAGANIN TYPHOID (SHAWARA) 


Assalamu alaikum warahmatullah ta'ala wabarakaatuh jama'a ƴan uwa maza da mata masoyana mabiya shafina na Shehudiezer daga ciki da wajen Nigeria ina yimuku fatan alkhairi duniya da lahira, Allah yasa muyi kyakkyawan qarshe ya bamu cikakkiyar lafiya a rayuwarmu

 Yau na zo muku da maganin TYPHOID (SHAWARA) domin masu fama da matsalar nan kokuma masu ƴan uwan da suke fama da matsalar.

Da farko dai zamu yi taqaitaccen bayani akan ciwon Typhoid daga qarshe kuma zan baku magunguna har guda biyu 

ALAMOMIN CUTAR TYPHOID👇

Alamomin wannan cutar suna bayyana ne a sati 1 zuwa 2 bayan kamuwa, ga kaɗan daga cikinsu👇

1- Zazzabi Mai zafi (39°c zuwa 40°c) Kuma baya sauka, kusan kullum haka mai wannan ciwon zai kasance, masamman in ba'a nemi magani da wuri ba ko ba'a nemi magani mai inganci ba.

2- Ciwon Kai 

3- Ciwon ciki.

4- Kasala da nauyin jiki.

5- Tari

6- Quraje qanana ko manta.

7- Shan wahala wajen yin bahaya.

Waɗannan sune manyan alamomin ciwon Typhoid.

ILLOLIN CUTAR TYPHOID👇 .

Duk matsalolin na faruwa ne ga waɗanda basu magance cutar dawuri ba kokuma waɗanda suka yi amfani da maganin da bashi da inganci, ga manyan illolin wannan cutar👇

1- Zubar jini ta ciki (internal bleeding).

Koda yake baya girmama sai dai yana Sanya baqin kashi. Amma Kuma zubar jini , Yana kawo qarancin jini

2- Idan har aka yi sakaci yana kaiwa matakin da dole sai an yi dashen hanji kokuma anyi operation Allah ya kiyaye

3- Tsallakawar qwayoyin cutar daga hanji zuwa cikin jini (peritonitis, sepsis) wannan na janyuwa izuwa ga taɓuwar sauran sassan jikin ɗan Adam har yakai ga mutuwa a qarshe Allah yatsare mu.

Su waye suka fi yiwuwar kamuwa da ciwon typhoid??

1- Yara qanana sun fi fargabar yiwuwar kamuwa da ciwon typhoid saboda raunin garkuwar jikin su hakan yasa sukafi saurin kamuwa da cutar, duk da haka kuma alamunta bai cika tsananta ga yara ba akan manyan mutane.

2- Rayuwa kokuma ziyartar yankuna kan iya kawo yiwuwar kamuwa da cutar, misali ;

Ziyartar Indiya ko zama a India 
Ziyartar Africa ko zama a Africa
Ziyarta ko zama a Kudanci da Gabashin Asia
Zama a Kudancin America ko ziyarar gururuwan


3- Rashin tsaftar Abinci

Rashin tsaftar Abincin da ake ci.
Rashin tsaftar Muhalli ko wurin zama ko wurin barci.
Rashin tsaftar ruwan sha.
Rashin tsaftar Kayan marmari kokuma amfani da waɗanda suka lalace, fruit irin su mangwaro da kankana da lemu da ayaba da abarba
Rashin tsafta ko kyan Ganyayyaki.


SHAWAR WARI A TAKAICE:

1- A dinga neman magani ingantace.

2- A dinga yin rigakafi daga wannan ciwon

3- A dinga ziyartar masana kiwon lafiya domin samun shawarwari da sauransu.

4- Kula da tsaftar Abinci ko abin sha .

5- A dinga wanke hannu kafin cin abinci ko shan abin sha .

6- A daina yin kashi ko bahaya a bainar jama'a kokuma a daina yin kashi a fili inda jama'a zasu gani ko su shaqa.

In an kiyaye waɗannan abubuwan insha Allah an kiyaye kai daga kamuwa da wannan ciwon na Typhoid.

Jama'a yakamata mu hankalta musan ciwon kan mu, musani ita lafiya guda ɗaya ce kiwonta ake yi idan karasata wallahi duk gatanka ba mai baka ita sai Allah, a dinga neman magani.

Wannan shine sirrin maganin Taipot ne wato shawara yawancin al'umma Tana musu illah wallahi, wasu suna da ita sun sani wasu kuma basu san sunada ita ba, kuma tana wahaldasu matuka, musamman a lokacin damana da lokacin bazara ko lokacin kaka

To domin kasan kanada ita ko bakada ita ka jarraba wannan sirrin zaka gane insha Allah ta'ala👇👇

To asamu waɗannan ganyayyaki kamar haka👇

1- Ganyen adurku 

2- Ganyen yandi  

3- Ganyen cheɗiya 

4- Ganyen namijin gurjiya( kurya), ba gyaɗa🥜 ba, ganyen gurjiya daban yake

5- Ganyen dogon yaro (bedi)

Note (akula): waɗannan ganyayyakin ana samunsu a ko ina, kuje kasuwa a tambayi malaman gargajiya masu siyarbda ganyayyaki da itatuwan gargajiya, kuma za'a iya siyowa a wurinsu in baza'a iya ebowa ba.

In an samu ganyukannan sai a shanyasu su bushe sai a jajjagasu ma'ana a daddakasu gaba ɗaya, sai a samu ruwa kamar galam biyu sai a juye ruwan a tukunya, sai a tafasa da ganyukannan yatafasa sosai sosai sai a sauke sai a nemi mayafi wanda iska ba zai shiga ba sai ka sunkuyarda kanka akan tukunyar sai kalullube kanka da wannan mayafin sai ka dinga jujjuya ruwan tukunyar da tsinke haka kokuma icce qarami haka kaɗan kaɗan turaren da suracin yana bugan jikinka da fuskarka, sai tiririn ya gama buganka sai ka buɗe kanka, idan ruwan ya huce saika ebi ruwan da hannunka ɗaya kasha sau 3 saika nemi wani baho ko roba haka ko bokiti sai ka juye ruwan a ciki sai kaje kayi wanka dasu gaba ɗaya, kullum kayi haka har kwana 3.

To Insha Allah in dai akwai shawara a jikinka to wlh zakaga wani zufa mai yauqi yana fitowa a jikinka ayayinda kakeyin turaren kokuma daidai lokacinda kagama, shine tabbacin kanada Typhoid (shawara), to amma in dai aka yi kamar yanda nace kuma kwana ukun to an rabu da ita insha Allah ta'ala indai TYPHOID ce.

Domin qarin bayani kokuma buqatar wani aiki daya shafi rayuwarka ko damuwarka kakirani a wannan numbobin 08136560680, 09020132884 in bata shigaba kayi magana a WhatsApp 08136560680

Domin tattaunawa da shehudiezer 👇

Facebook 👉 fb.me/shehudiezer 

Instagram 👉 ig.me/shehudiezer

WhatsApp👉 wa.me/2348136560680Wannan sirrin Hadiyyace daga Jikan Dottiwa mai Inyass Allah yasakamasa da alkhairi, kuyiwa annabi salati 10 kuma kayi sharing inda halin hakan
Next Post Previous Post
2 Comments
  • Anonymous
    Anonymous July 13, 2022 at 5:42 AM

    Mutarimuhammad

  • Anonymous
    Anonymous August 20, 2022 at 3:25 AM

    Masha Allah Allah taala ya saka da alheri

Add Comment
comment url