Yadda Zaka Samu Kuɗin Kashewa Kullum

YADDA ZAKA SAMU KUƊIN KASHEWA KULLUM TA HANYAR ADDU'A 🤑💵💵A'uzu billahi minash shaidanir rajim
Bismil lahir rahmanir raheem.
Assalamu alaikum warahmatul Lahi ta'ala wa barakatuhu ƴan uwa maza da mata ahlullahi masoya Manzon tsira annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallam nagida dana waje, na Nigeria da na qasashen waje, dafatan kuna lafiya, Allah yasa haka ameen.
Allah ya qaramana lafiya yabamu yanda zamuyi hidindimun rayuwarmu har abada.

Wannan posting din na yanda zaka samu kuɗin kashewa kullum yau zan yishi ne domin marasa hali da wadanda suke cikin qunci da tsananin talauci basuda hanyarda zasu samu wani abu kokuma lalura ta hana, wannan posting din jama'a da dama daga wurare daban daban da garuruwa daban daban suna tambayata wai malam shin babu wata addu'arda za'a taimakamana da ita acikin kundinku wadda mutum zai dinga yinta a koda yaushe idan yana son Allah ya dinga bashi rufin asirinda zai dinga samun kudinda zai dinga kashewa yana biyan qananan buqatunsa na yau da kullum?
To jama'a waɗanda suke yimana wannan tambayar yau dai nazomuku da amsa harda guzuri. Eh tabbas akwai domin Allah ya tabbatarmana acikin Alqur'ani da hadisai cewa shine mai bayarwa kuma shine mai hanawa, kuma idan ka roqeshi ya tabbatar cewa zai amsamaka, kuma ya fadi irin salonda ake roqonsa da sunaye da abubuwanda ake kiransa dasu ya amsa, Allah ne Ubangijinmu shine gatanmu kuma shine ya haliccemu kuma shine ya gayamana mu roqeshi zai karbi addu'o'inmu, da wannan nake tabbatarwa ƴan uwana maza da mata cewa wallahi ku kwantarda hankalinku tabbas Allah baya rowa kuma baya qin bayinsa baya barin bayinsa a wulaqance saidai idan sune sukabar kansu a wulaqance.

To da farko dai shi talauci musiba ne bala'i ne kuma tashin hankali ne fitina ne yana haifarda baqinciki da baqin jini da hawan jini, wani lokacin ma yakan kai mutum zuwa halaka idan mutumin ba mai qarfin imani bane, Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama wanda shine masoyi na Allah wanda babu kamarsa, makusanci ne na Allah subhanahu wata'ala wanda idan ya ɗarsa abu a ransa Allah zai zartarmasa shi, Annabi dakansa kusan kullum sai ya nemi tsarin Allah daga talauci da kafirci, akai akai yana yawan neman tsarin Allah daga musibar talauci, kuma Annabi ya umarci mutane da cewa su yaqi talauci kada mutum yabari talauci ya raɓeshi domin musiba ne, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam baitaɓa bari talauci yayi galaba akansa ba, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yayi hidindimu dayawa da ayyuka dayawa da zirga-zirga ta neman halak dakuma rabuwa da talauci dayawa, tin yana yaronsa baitaɓa bari talauci yayi tasiri akansaba har yagirma, to kunga Annabi dakansa ya yaqi talauci yazama wajibi muma masoyansa mabiyansa al'ummar sa muyaqi talauci muyi addu'a munema daga falalar Allah domin ya tausayamana yabamu arziqi daga arziqinsa da bashida iyaka domin murabu da talauci kokuma kar mudinga zama da talauci, domin wallahi zama da talauci babban tashin hankali ne, ga yadda za'ayi aikin👇

ana son mutum wanda zaiyi wannan wuridin ko aikin ya kasance yanada tsarki a duk lokacinda zai yi wannan wuridin, sannan kuma anaso mutum yayi alwala, kuma Idan son samune anfi son mutum yadinga yin addu'ar a cikin masallaci domin addu'a tana karbuwa sosai acikin masallaci domin masallaci kamar nan ne dakin Allah a hausance kenan, kokuma ana so adinga yin wannan wuridin inda ba hayaniya saboda addu'a bata haɗuwa da hayaniya da maganganu, idan ancika wadannan sharuddan anyi alwala shikenan, to bayan kayi alwalla Kaje masallaci kokuma kaje ka zauna a inda yakeda tsarki kuma ba hayaniya agurin sai kayi;

(1) Nafila raka'a biyu (2), Istigfari qafa ɗari (100), Salatin Annabi qafa ɗari (100), La ilaha illallahu qafa ɗari (100), bayan kagama wannan sannan kafara wuridin 👇
 “Waman yattaqil laha yaj'al lahu makhrajãã wa yarzuqhu min haisu lãã yahtasib waman yatawakkal alallahi fahuwa hasbuh innallaha baligu amrihi qad ja'alallahu likulli shai'in qadraa” qafa ɗari uku da sha uku (313), bayan kagama karanta wannan ayar daidai yanda nafaɗa sai kakaranta;
Wallahu galibun alãã amrihi qafa ɗari huɗu da hamsin (450), bayan kagama wallahu galibun alãã amrihi qafa ɗari huɗu da hamsin sai kayi addu'a ka roqi Allah buqatar yabaka kudi wallahi tallahi indai kayi imani a zuciyarka kuma kayi Tawassuli kayi wannan aikin da kyakkyawar niyya wallahi zaka samu kudi aranar ta hanyarda bakayi tsammani ba, Allah zai sa kasamu kudi ta inda bakayi tsammaniba, Allah bazai barka kawuni baka samu ko naira ba, kuma idan ka dage dayin haka kullum, wallahi mai arziqima bazai nunamaka qawa zuciba da farin cikin rayuwa da kwanciyar hankali, domin kai kullum zaka samu daidai wanda zakayi lalurorinka kuma Allah zai qaramaka imani da godiyar Allah, zaka kasance kanada godiyar Allah, rayuwarka zata kasance cikin kwanciyar hankali.
Allah yabada ikon yi kuma Allah ya yaye mana talauci duniya da lahira Allah yarabamu da babu, yarabamu da qunci da takaici da hawan jini da baqin cikin rayuwar duniya da lahira yan uwa.

Domin neman ƙaarin bayani kokuma masu neman ayimusu wani aiki na karya sihirii ko mallaka ko wacce takeson yin aure ko maganar kasuwanci, kokuma aiki wanda ya shafi rayuwarsu kokuma lafiyarsu ko mu'amalarsu sai su tuntubeni akan numbobin wayata kokuma akan WhatsApp a wadannan numbobin namu naqasa👇
09020132884

Duk Wanda yakeda tambaya sai yayi comment da tambayarsa kokuma yakiramu awaya a wannan numbobin 08136560680, 09020132884, Allah yasa mu dace duniya da lahira ameen.

Bayan haka ina neman addu'ar ƴan uwa nagama makaranta University kuma cikin ikon Allah na gama National service kwanakinnan, Allah yabani aikin yi Allah yakawomun babban rabo, Allah ya taimakemu baki daya amin
Bayan haka ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
Tiktok: 
YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka masu ijaba sosai dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa

Alhamdulillah

08136560680 (WhatsApp)
09020132884
Domin tambaya kayi comment aqasa kokuma akira waya. Allah shine mafi sani
Next Post Previous Post
12 Comments
 • Unknown
  Unknown September 19, 2019 at 11:54 AM

  Wallahi tana aiki,ba'a gwada sosai,Allah ya saka da alkhairi

 • Unknown
  Unknown October 24, 2019 at 10:10 AM

  Mashallah

 • nasiru
  nasiru August 16, 2020 at 6:43 AM

  yaya huridin akeyi da hausa

 • Ali mah zaurey
  Ali mah zaurey September 22, 2020 at 8:57 AM

  HABA?

 • Ayuba basher
  Ayuba basher April 19, 2021 at 2:59 PM

  Muna godiya allah ya kara sani

 • Unknown
  Unknown September 8, 2021 at 5:30 AM

  Ya akeyin wuridin da hausa

 • Muhammad
  Muhammad November 2, 2021 at 3:21 PM

  Sakallahu qairan
  Masha Allah

 • Unknown
  Unknown December 27, 2021 at 12:52 AM

  Munagodiya allah yaqara basira da hazaqa

 • Unknown
  Unknown December 28, 2021 at 11:04 AM

  MASHA ALLAH

 • Unknown
  Unknown January 15, 2022 at 6:50 AM

  Masha Allah sai godiyan Allah.

 • Unknown
  Unknown February 27, 2022 at 4:23 PM

  Allah yakabudi

 • Unknown
  Unknown February 27, 2022 at 4:24 PM

  Allah yabada Mai yawa

Add Comment
comment url