Maganin Ciwon Ciki Nantãke

MAGANIN CIWON CIKI NAN TAKE


Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu 
Barkanmu da warahaka yan'uwa maza da mata musulmai masoya Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam na Nigeria, Niger, Cameroon, Chad, Mali, Togo, Benin Republic, Cotonou, India, United States of Anerica, masoyana na qasar France da da dukkanin masoyana na duniya dafatan kuna cikin qoshin lafiya, Allah yasa haka ameen, Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya, Allah ya tsaremu daga dukkanin sharri da bala'i da musiba, Allah ya jiqan iyayenmu da kakanninmu da makamanmu wadanda suka rigamu gidan gaskiya, Allah yarabamu da Talauci duniya da lahira, Allah yasa mizaninmu ya cika da alkhairi alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallam, Allah ya rabamu da wuta da radadinda, Allah yahaɗamu da Aljanna da rahamarta da jindadinda yake cikinta, ya Allah ka shayar damu imani da iliminka, ka qaramana kwanciyar hankali Ameen..


Kamar yadda na yimaku bayani akan cewa zan gayamaku yadda akeyin maganin ciwon ciki kokuma murdawar ciki idan Allah ya jarabci mutum da shi to Insha Allahu yanzu zanyi taqaitaccen bayani akansa kuma Insha Allah idan kuna biye dani kunyi saving din wannan page ɗin nawa na shehudiezer.com agaba zan yi cikakken bayani kokuma ince zan kawo muku babban sirri na maganin ciwon cikin Insha Allah, amma kafin nan, ga maganin ciwon kai wanda muke magana akansa a wannan post ɗin yanzu 👇


A farko dai ciwon ciki ya rabu zuwa bangarori daban daban, a gurguje zan kawo wasu daga cikin rabe raben ciwon ciki wadanda mutane suke yawan fama dasu, gasunan 👇

1-Ciwon ciki wanda Allah yake dorawa mutane: Shi wannan kalar ciwon cikin shine wanda yake samun mutum kwatsam, ba tareda wani dalili ba, kokuma mutum ciwon ciki ya sameshi idan yaci abinci ba daidai ba kokuma yayi haɗe haɗen abinci wanda bai kamata ba, kokuma yaci abinci da yaji kokuma yaci abinci wanda yakeda maiqo kamar su Awara, Qosai, Dankali, Alale da sauransu, dadai duk wabi kalar ciwon ciki wanda ba zaici karo da sauran misalai da zamu kawo aqasa ba.

2- Ciwon cikin Al'ada na mata: Wannan shine ciwon ciki wanda jinin al'ada na qarshen wata ne wanda mata sukeyi yake sakawa wasu daga cikin mata ciwon ciki.

3- Ciwon cikin sihiri ko ture: Shi wannan kalar ciwon ciki shine wanda yake samun mutum arasa gane kansa, asha magani amma yaqi bari, irin wannan ciwon ciki yana samun mutum ne idan anmasa sihiri kokuma idan aka yiwa mutum barbaɗen wani abu na sihiri yaci ba tareda ya saniba ko idan aka turowa mutum aljani ya yimasa ajiyar sihiri a cikin cikinsa, kokuma idan aka yiwa mutum sihirin ture wanda za'a sakawa mutun ciwon ciki nan take, da sauransu.
Wannan sune manya manyan abubuwanda suke kawo ciwon ciki, ga maganin👇


Da farko dai zaka samu ruwan Zam Zam, kokuma tsarkakakken ruwa, sannan ka tofawa ruwan “LALABISA FEE BAƊNIHEE ILA YAUMI YUB'ASUUN” Qafa arba'in da ɗaya (41), bayan angama tofawa, sannan idan kaine bakada lafiya sai kayi salati kasha wannan ruwan da akayi tofin, idan kuma wani ne cikinsa yake ciwo kokuma wata ce cikinta yake ciwo bayan yayi salati ga Annabi sai yasha ruwan tofin, wannan kenan

Ga wani maganin ciwon ciki amma na rubutu 👇

Ana rubuta “LALABISA FEE BAƊNIHEE ILA YAUMI YUB'ASUUN” da tawwada shima kamar dai na tofin qafa arba'in da daya amma banbancinsu kawai shine wannan rubutawa za'ayi, za'a rubuta a wanke ahada da Zuma asha, idan kuma Zuma bata samuba babu matsala ana iya shan rubutun ahaka Insha Allah.

Idan kuma marar lafiya ne cikinsa yakemasa ciwo yana kwance kokuma bazai iya yi dakansa ba sai a rubutamasa ayar qafa bakwai (7) ajikin farar takarda anaɗeta ayimasa laya aɗaura masa aciki Insha Allahu cikinsa zai daina ciwo, Allahu a'alam.

Bayan haka ƴan uwa maza da mata ya kamata mu dinga tinawa cewa Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya sanar damu cewa zuma tana maganin ciwon ciki idan mutun cikinsa ya fara ciwo Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agaresa yace idan ya sha zuma cikin zai daina ciwo, kunga kuwa ya kamata muyi amfani da sirrinda ya fito daga bakinda baya qarya bakin fiyayyen halitta shamaki a fadar Allah farin jakada mai raba aljannah. Allah ya qarawa annabi daraja ameen

Allah yabaiwa dukkanin marasa lafiyarmu na gida Da na asibiti lafiya amin, kuma Allah yabamu sa'a Allah yatemaki musulunci da musulmai ya qasqanta kafirci da kafirai, Allah yatsaremu daga sharrin masharranta da maqiya da mahassada da Aljannu da Iskokai da Dukkan abun qi, Allah kabamu zuri'a ɗayyaba da mata naqwarai, mata kuma Allah yabasu mazaje nagari.

Domin neman ƙarin bayani kokuma masu neman ayimusu wani aiki na karya sihiri ko mallaka ko wacce takeson yin aure ko maganar kasuwanci, kokuma aiki wanda ya shafi rayuwarsu kokuma lafiyarsu ko mu'amalarsu sai su tuntubeni akan numbobin wayata kokuma akan WhatsApp a wadannan numbobin👇
09020132884

Duk Wanda yakeda tambaya sai yayi comment da tambayarsa kokuma yakirani awaya 08136560680, Allah yasa mudace duniya da lahira ameen.

Ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa

Next Post Previous Post
7 Comments
 • Unknown
  Unknown September 19, 2019 at 11:56 AM

  Muna godiya malam,Allah yaqarsa basira

 • Unknown
  Unknown September 19, 2019 at 11:59 AM

  Muna godiya malam,Allah yaqarsa basira

 • Shehudiezer
  Shehudiezer September 19, 2019 at 4:21 PM

  Ameeen ameeeen

 • Fatima usman
  Fatima usman September 24, 2019 at 6:51 AM

  Wannan maganin Nagwada yayi Allah yasaka da mafificin alkhairi

 • Unknown
  Unknown September 25, 2019 at 3:01 PM

  Ammafa yana aiki, allah yataimaka

 • Shehudiezer
  Shehudiezer October 23, 2019 at 3:42 AM

  Good medicine

 • Unknown
  Unknown November 28, 2021 at 6:54 PM

  Allah yasaka da alkhairi

Add Comment
comment url