Maganin Ciwon Kai Sahihi

YANDA AKE KAMUN KAI IDAN KANKA YANA CIWO




Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu
Tsira da amincin Allah suqara tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wa sallama, Allah Ubangiji yasa mugama da duniya lafiya, Allah kasa muyi kyakkyawan qarshe Allah yasa nusamu sakamako mai kyau na Aljannatul firdausi.
Jama'a masu bibiyarmu masoya Annabi Sallallahu alaihi Wasallama na ciki da wajen Nigeria ina yimaku fatan alkhairi Duniya da lahira

Yau dai bayaninmu ne akan abunda yashafi ciwon kai ne da zafin kai
Ciwon kai ya rabu kashi-kashi, akwai ciwon kai wanda Allah ne yake dorawa bayinsa, Ɗaya daga cikinsu akwai wanda zirga zirga ce da hayaniya da wahala da pressure da ɗawainiya ne suke ɗorawa mutum shi, misali idan mutum yashiga cikin hayaniyar jama'a kokuma yashiga mota yayi bulaguro qarar kota da iskan mota zai iya ɗorawa mutun ciwon kai, kokuma mutum yayi gudu ko yayi noma kokuma yayi wani aikin wahala, wadannan misalai ne na abubuwanda zasu iya dirawa mutum ciwon kai, haka zalika akwai ciwon kai na rashin lafiya wanda rashin lafiya ce zata sakawa mutum ciwon kai, misali idan mutum yana fama da ciwon Malaria zazzabin cizon sauro kokuma idan mutum yana fama da Mura ko Tari, mura da tari idan mutum yana fama dasu tabbas sune mafi yawancin abubuwanda suke sakawa mutane ciwon kai musamman a lokacin sanyi da lokacin damana , wadannan suma wasu hanyoyi ne da mutum zai iya tsintar kansa da da ciwon kai.
Haka zala sai ɓangare na qarshe wanda shine bayani na qarshe akan rabe raben ciwon kai, shine Ciwon kai wanda mutum zai iya samu ta hanyar sihiri ko jifa ko makaru ko ture, za'a iya jifar mutum da ciwon kai kokuma ajefeshi da wani abinda zai dinga doramasa ciwon kai ko ciwon/hali/yanayinda zai dinga sakawa mutum ciwon kai, idan namijine misali za'a iya jifarsa a kasuwancinsa ko a jefeshi a harkar aikinsa ko siyasarsa kokuma jindadin rayuwarsa ko tsakaninsa da iyalansa ko iyayensa ko mai gidansa, to wannan zai iya janyowa mutum ciwon kai.
Idan macece kuma za'a iya jifarta domin a lalata tsakaninta da maigidanta kokuma tsakaninta da samarinta kokuma a jefi kasuwancinta kokuma ayimasa sihiri domin a mallaketa kokuma domin a juyo hankalinta kokuma domin wani abu daban, kokuma idan mai aurece kishiyarta zata iya jifanta domin ta bata tsakaninta da mijinsu kokuma tasa mijinta ya tsaneta kokuma tasa mijinta yadaina sonta kamar yanda yake son wacce tasa ayi jifan, kokuma wata tawaje tayimiki sihiri domin tasaka mijinki ya koreki kokuma ya sakeki ko kudinga faɗa da masifa, wannan ko kishiryarki zata iya yin haka tabbas, sannan kuma shifa ciwon kai yana daga cikin manya manyan alamomin sihiri a jikin mutum, yawan yin ciwon kai yana daga cikin manya manyan alamomin da suke nuna cewa mutum yana fama da sihiri ko jifa, 
Inshaallah Yanzu zanyimuku bayanin akan yanda ake (kamun kai) a musulunce👇

Idan wacce zaka yiwa kamun kan MACE ce (muharramarka) ga yanda zaka gudanarda aikin👇,
Dafarko zaka karanta Fatiha qafa 1, sai kayi salatin annabi qafa 3, sai kadora kanka akan goshinta kamatse sosai sai kasaake karanta Fatiha qafa (7), qulhuwallahu qafa (3), falaqi qafa (3), nasi (3) bayan haka sai kakaranta LAQAD JÃ'AKUM RASULUN MIN ANFUSIKUM......har zuwa qarshe qafa (3), hasbunallahu wa ni'imal wakeel qafa bakwai (7), aamanarrasulu qafa (3), Aayatul kursiyyu qafa (3), salatin Annabi, kokuma Salatil fatihi qafa bakwai (7), sannan sai ka jawo hannunka kamatse a hankali kajawo hannuwanka har sai sun hadu, Insha Allahu wannan ciwon kan ya rabu da ita kenan, Allah shine mafi sani.

Idan kuma MACE ce wacce BA MUHARRAMARKABA ga yanda zaka yimata aikin👇
zaka tofa dukkan abunda zaka karantamata kamar yadda nayi bayani abaya,to za'a tofamata ne a Ruwa tasha kuma tawanke fuskanta sannan kuma tashafa ruwan tofin a goshinta, a mman kuma salatil fatihi qafa ɗari da sha ɗaya (111), za'a tofa shine bambanci, akula sosai... insha Allah zai daina batareda shan wahalaba.

Idan kuma NAMIJI NE ga yanda za'ayi 👇
Zaka kama kansa kamar yadda nayi bayani a chan sama abaya sannan kakaranta Fatiha qafa bakwai (7), Qul huwallahu qafa bakwai (7), Falaqi qafa bakwai (7), Nasi qafa bakwai (7), Salamun qaulan min rabbin rahim qafa (7), La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem qafa bakwai (7), hasbunallahu wa ni'imal wakeelu qafa (11), Salatil fatihi ko salatin annabi qafa (3), Insha allahu za'a warke, kan zai daina ciwo.
Bayan haka Insha Allahu zamu cigaba dayin bayani akan magungunanda Allah yahoremana acikin alqur'ani da sunnah, da dukkanin sirrukanda basu saɓawa addinin musulunci ba Insha Allah.. Allah yabani ikon gabatarwa, kuma Allah yabawa dukkan marasa lafiyarmu nagida Dana asibiti lafiya ameen, kuma Allah yabamu sa'a Allah yataimaki musulunci da musulmai ya qasqanta kafirci da kafirai, Allah yatsaremu daga sharrin masheranta da maqita da mahassada da Aljanu da Iskokai da Dukkanin abun qi, Allah kabamu zuri'a ɗayyaba da mata na qwarai, mata kuma Allah kabasu mazaje nagari.

Domin neman qarin bayani kokuma masu neman ayimusu wani aiki na karya sihiri ko mallaka ko wacce takeson yin aure ko maganar kasuwanci, kokuma aiki wanda ya shafi rayuwarsu kokuma lafiyarsu ko mu'amalarsu sai su tuntubeni akan numbobin wayata kokuma akan WhatsApp a wadannan numbobin👇
09020132884

INSHAALLAH ABUNDA ZANYI BAYANI AKANSA AGABA SHINE ZAN GAYAMAKU YANDA AKEYIN SIRRIN MALLAKA DA JUYODA HANKALIN MIJI, FIRAQU, JALABI DA DAFA'I, DA MAGANIN CIWON CIKI DAKUMA TASHIN ZUCIYA.

Ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa

Alhamdulillah

Next Post
6 Comments
  • Unknown
    Unknown September 6, 2019 at 1:11 PM

    Masha Allah Allah yasa alkhairi dan uwa insha Allah zamu gwada

    • Shehudiezer
      Shehudiezer September 6, 2019 at 1:26 PM

      Ameeen

    • Unknown
      Unknown September 19, 2019 at 11:53 AM

      Hausa malam

  • Fatima usman
    Fatima usman September 24, 2019 at 6:48 AM

    Masha Allah

  • Unknown
    Unknown September 25, 2019 at 3:00 PM

    هذا صحيح،شكرا

  • Unknown
    Unknown October 24, 2019 at 10:08 AM

    Alhamdullah

Add Comment
comment url