Yadda Ake Karya Sihiri Original

YADDA AKE KARYA SIHIRI KO ASIRI ORIGINAL 


Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu masoya kuma ƴan uwana maza da mata al'ummar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam, dafatan kuna cikin qoshin lafiya kuka kun wuni lafiya, Allah yasa haka ameen.
Bayan haka yau dai Insha Allahu zan yimuku bayani ne akan yadda ake karya Sihiri, ko Tsafi, ko sammu, ko Asiri, ko Tsubbu, ko Ture, ko duk wani abunda ya shafi mugun magani, ko mugun baaki, da fatan kuna biye dani ɗari bisa ɗari.
Shi dai sihiri abu ne wanda ya zama ruwan dare acikin al'ummar mu ayanzu, ƴan baqin ciki sunyi yawa mahassada sunyi yawa maqiya sunyi yawa waɗanda basa tsoron Allah sunyi yawa.

Tayaya zakasan anmaka sihiri? ga Amsa👉:

Mafi yawancin malamanmu na yanzu sun iya jefawa mutum sihiri, jifar mutum yazama abu wanda bashida wahala, kuma ya kasance idan aka jefi mutun yakan shiga mummunan hali ko yashiga matsala wacce bai saba shigarta ba kokuma ince bai taɓa shigarta ba, ana iya jifar kasuwancin mutum, ana iya jifar farin jinin mutum, ana iya jifar auren mutum ana iya jifar farin cikinda mutum yake ciki, ana iya jifar karatun mutum na boko ko na addini, ana iya jifar lafiyar mutum, ana iya jifar wata baiwa da aka ga Allah ya baiwa wani mutum, ana iya jifar kasuwancin mutum ko shagonsa, ana iya jifar gangar jikin mutum ana iya jifar cikinda mace take ɗauke dashi ana iya jifar ƴaƴanki ko ajefi kyakkyawar alaqarda take tsakaninki da mijinki tazama mummuna kudinga faɗa kokuma ya chanza miki, ana iya jifar mutum yadaina zama guri ɗaya, ko yadaina zama gurin kasuwanci ko office ko wurin aikinsa, ana iya jifar mutum asaka masa kasala da nauyin jiki ya kasa yin komai na kirki, wadannan dukkaninsu kaɗan daga cikin jifarda ake iya yiwa mutane ne, akwai iri irin jifa da ake yiwa mutane sunfi dubu, kuma akan komai ana iya jifar mutum.

Idan kuma har aka jefi mutum koma wane irin jifa ne kuma aka samu nasara to tabbas hakan zai taɓa wani bangaren farin cikinsa ko lafiyarsa ko ni'imarsa, saboda gudun kasancewa dumu dumu acikin sihiri anyimaka sihiri amma karasa yanda zakayi ka karyashi kokuma kanemi magani ko makarinsa ko tsari daga gareshi, wannan ne babban dalilinda yasa na kawomuku wannan aikin na karya sihiri mai rai ne wannan aikin wallahi yana aiki ba shakka ko makawa akansa, ga yanda aikin yake👇
1- Da farko dai ana son kasamu (allon qarfe), Allon qarfe wani allo ne ɗan karami kamar girman littafi exercise book, ana siyar dashi awurin masu walda, in kaje kacemasu suhaɗamaka allon qarfe, zasu hadamaka kokuma ka nemi aro agurin wanda kakega zaka samu allon agurinsa.
2- Ana so akunna wutar garwashi acikin (mangal) ,or (makubur), ma'ana abunda ake dafa abincin da wutar garwashi dashi, kokuma a hura wutar gawayi a bakin murhu (ammafa idan za'a iya zaunawa akusa da murhun ayi wuridin). Bayan ka hura wuta👇
3- Sannan sai karubuta (ya qahharu) kamar yadda kake gani acikin hotonda yake qasan rubutunnan👇 sai ka rubuta sunan wanda akeso ASIRIN KO TSAFIN yafita ajikinsa Asama sannan kuma karubuta sunan nasa aqasa, ma'ana acikin wannan babban (ha'un) ɗin zaka saka sunan NASA Asama da qasa, amma fa da larabci zaka rubuta misali idan Muhammad ne sunan wanda akeso ayiwa wannan maganin sai karubuta Muhammad da larabci, idan baka iyaba kanemi wanda ya iya rubutun larabci ya rubutamaka, gashi kamar haka👇

4- Sannan kai kuma wanda zakayi wuridin kayi alwala sannan kazo ka ɗauko wannan allon da kayi wannan rubutun sai ka aza dai dai inda rubutun yake akan wuta ya dinga kallon wutar, ma'ana wutar tana qona allon da zafi, kai kuma sai kafara wuridinka kayi tayi har sai ka gama sannan kaɗauke allon akan wutar, za'ayi wuridin ne na Ya qahharu bayan anɗora allon akan wutar, za'ayi wuridin ya Qahharu qafa dubu goma sha biyu (12,000) kuma za'a iya taya mutum yin wuridin, kokuma kasamu waɗanda zasu kamamaka ayi wuridin ahaɗa qafa dubu sha biyu ɗin.
Note, Akula: zaku iya yin wuridin ko Ku nawane matuqar kunada tsarki, ma'ana ba mutum ɗaya kadaine zai iya yin wuridin ba.
Sannan kuma dole ne wadanda zasuyi wannan wuridin sunada tsarki kuma sau ɗaya akeyin wannan wuridin, kuma ana yiwa mahaukaci, anayiwa wanda kowane irin ciwone yasameshi Insha Allahu.
Da yardar Allah idan dai har kunyi wannan wuridin daidai yadda aka gaya muku, to magana ta qare, InshaAllah kowane irin SAMMU ko TSAFI akayiwa mutum, to Da kunyi masa wannan wuridin, da yardar Allah indai har kunyi daidai to kowane irin sihiri ne kafin kwana bakwai (7) zakuga SIHIRIN yafara fita ajikinsa idan dai har kunyi yanda aka gayamaku, domin wannan abun babu shakku akansa, shine aiki mafi sauqi Wanda kowa zai iya yinsa a bangaren karya TSAFI ko SIHIRI,kuma wallahi nida kaina nayi wannan babban wuridin kuma naci babbar nasara akansa, aikin yayi kyau sosai kuma ya taimakeni kuma yayimun tasiri.
Kowa zai iya yin wannan wuridin, mace ko namiji, matar Aure ko budurwa, matar Aure zata iya bayarwa ayimata, kokuma tabani inyimata ga NUMBATA duk mai buqatar qaarin bayani, kokuma yakeso ayi masa kokuma ayiwa wani Dan uwansa, to yanemeni awaya kokuma YAYIMUN MAGANA TA WHATSAPP👇
09020132884
Amma fa duk Wanda za'a yiwa to lallaine zai biya kuɗin sadaqa abunda ya sauwaqa, yauwa, Allah yasa mudace, kuma Allah yasa ayi daidai, kuma Allah yasa ayi nasara akan abunda ake buqata.
Sannan kuma bugu da qaari akwai waɗansu magunguna kala-kala acikin wannan shafin nawa idan kunyi aqasa kokuma kunyi sama zaku kallesu, kuma kuyi saving din bookmark na page ɗin nawa a browser dinka domin duba new update a page din
Kuma mun bude YouTube Channel, duk wadannan abubuwan da kuka ga muna yin bayaninsu anan to acan zamu fara sakasu zaku kalli yanda ake yin practical dinsu DALLA DALLA acikin YouTube Insha Allah, zaku kalli aikin a VIDEO ba a rubuce ba.

Wannan shine link na YouTube Channel dina, dan Allah kushiga suyi liking videos dina kuma kuyi subscribing kudanna qararrawa👇

Kuma duk Wanda ya gwada wannan sirrin bai yimasa aikiba to ya binciki kansa, kuma yayi comment domin in gayamasa inda yayi kuskure
Domin neman qarin bayani kokuma masu neman muyi musu wannan aikin na karya sihiri ko mallaka ko wacce takeson yin aure ko maganar kasuwanci, ko wacce take samun matsala da mijinta ko wacce aka shiga tsakaninta da mijinta ko ya saketa ko wacce take mugayen mafarkai ko yawan faɗuwar gaba ko tsoro, kokuma aiki wanda yashafi rayuwarsu kokuma lafiyarsu ko mu'amalarsu, koma wane irin aikine munayi, sai su tuntubeni akan numbobina kokuma akan WhatsApp a wadannan numbobin nawa👇
09020132884
Ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
Tiktok: https://www.tiktok.com/shehudiezer/
YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa
Alhamdulillah
Next Post Previous Post
20 Comments
 • FRIENDS MASU DARAJAH
  FRIENDS MASU DARAJAH October 3, 2019 at 4:22 PM

  Nice one

 • Shehudiezer
  Shehudiezer October 23, 2019 at 3:38 AM

  Nice

 • Unknown
  Unknown October 24, 2019 at 10:07 AM

  Yayi kyau

 • Unknown
  Unknown January 16, 2020 at 1:50 AM

  Mezaka dinga Fadi cikin wuridin?

  • Shehudiezer
   Shehudiezer July 4, 2020 at 4:42 AM

   Ya qahharu 12,000,kuma za'a iya taya mutum yi

 • Unknown
  Unknown July 27, 2020 at 8:33 PM

  Masha Allah.mlm Allah yasaka da alheri

 • Unknown
  Unknown August 18, 2020 at 1:46 PM

  Alhamdulillahi Allah ye bada lada ni ina famada masalannan Sosai kamar nawane abun sadakan inaso kayimun

  • Shehudiezer
   Shehudiezer January 14, 2021 at 3:26 AM

   Kamun magana a WhatsApp kokuma kikirani 08136560680

 • anonymous
  anonymous September 17, 2020 at 9:09 AM

  Bayan an gama wuridin an sauke allon akan wuta ya za'ayi dashi?

  • Shehudiezer
   Shehudiezer January 14, 2021 at 3:27 AM

   Ba abinda za'ayi dashi,kawai barinshi za'ayi

 • anonymous
  anonymous September 17, 2020 at 9:09 AM

  Bayan an gama wuridin an sauke allon akan wuta ya za'ayi dashi?

 • Ayuba basher
  Ayuba basher April 19, 2021 at 3:10 PM

  MUNGODE

 • Umar kakangi
  Umar kakangi April 27, 2022 at 10:36 AM

  Alhamdulillahi, Allah ya mana jagora, hakika wannan aikin na qahari yana aiki sosai ba kadan ba, domin wallahi abun dai sai wanda ya gwada domin mun dade muna aiki da shi kuma yana yi. Allah ya kara jagora

  • Shehudiezer
   Shehudiezer July 1, 2022 at 8:39 AM

   Ameen
   Haqqun
   والله على ما نقول وكيل

 • Anonymous
  Anonymous October 14, 2022 at 7:38 AM

  Alhamdulillah Allah yasaka da alkairi idan mutun shizaiyi dakansa fan? Zaibada sadaka awake kenan kuma sadakan Mai mutum zaiyi?

  • Shehudiezer
   Shehudiezer October 3, 2023 at 9:30 AM

   A'a, nabashi fisabilillahi

 • Anonymous
  Anonymous January 23, 2023 at 3:32 AM

  Allah yasaka da alkhairi Dr to malam idan nagamaaikin zan Iya Shan rubutan?

  • Shehudiezer
   Shehudiezer October 3, 2023 at 9:30 AM

   Aa

 • Anonymous
  Anonymous October 3, 2023 at 7:52 AM

  Nana

  • Shehudiezer
   Shehudiezer October 3, 2023 at 9:30 AM

   ??

Add Comment
comment url