Sirrin Dafa'i Da Mayarda Sharri Akan Maqiyi

SIRRIN DAFA'I DA MAYAR DA SHARRI AKAN MAQIYI
 Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu ƴan uwa maza da mata mabiya shafin shehu diezer na ciki da wajen Nigeria, maza da mata, yan uwa da abokanan arziqi ina miqa gaisuwa a gareku, na gaidaku, kwana biyu kun jini shuru ba posting ba bayani, to abubuwa ne suka yimun yawa matuqa ƴan kwanaki biyunnan, ku sakani a addu'a Allah yasa in samu aiki mai albarka.

Yau kuma na zo muku da da babban sirri na dafa'i, kariya daga ƴan baqin ciki da mahassada da maqiya da ƴan adawa da ƴan qyashi da magulmata da masu jifa da sihiri, na kawomusu magani ko ince kariya daga dukkanin sharrinda za'a iya turowa mutum ko a jefeshi ko a aikata masa, da kuma raddi da mayar da sharrin ko jifan ko sihirin ko makarun akan wanda yayi kokuma wanda ya sa ayi, Insha Allah wannan posting din da zanyi zai nunamuku yanda zaku yi wannan aiki cikin nustuwa da kwanciyar hankali , ga sirrin nan a qasa👇

GA SIRRIN MAIDA KAIDI GA MAQIYI KO MASHARRANCI MO MAHASSADI KO MAJEFI, JAMA'A MUKARE KANMU A RAYUWAR NAN SABODA WALLAHI WANNAN LOKACIN MAQIYA DA MAHASSADA SUNYI YAWA A RAYUWA,YANZU MUTANE AKE KIWO BA DABBOBI BA WANI ZAKAGA KODA ACE BAKU TAƁA MAGANA DASHI BA AMMA KUMA KAWAI HAUSHINKA YAKEJI A RAYUWA, BAYA SO YAGA CHI GABANKA KOKUMA BAYASO YAGA FARIN CIKINKA KO YAGANKA A CIKIN WALWALA KO BAYA MA SO YA GANKA, TO WANNAN SIRRIN DA ZAN BAYAR WALLAHI IN KA YISHI MUTUM IN YANA YIMAKA QULLE QULLE WALLAHI IN BAI DAINABA ZAI YI MUMMUNAR RASHIN LAFIYA KO YAMUTU.

Shi wannan sirrin ana yinsa ne kamar haka👇👇👇

Ana rubuta suratul Taubah (Barã'atu) qafa ɗaya (1) amma kuma duk qarshen kowace aya da ake rubutawa za'a rubuta 👇
“Wa raddal lahul lazina kafaru bigaizihim lam yanããluu khairaa, wakafal lahul mu'umininal qitããl, wa kããnal lahu qawiyyan aziza” qafa daya (1), sannan a rubuta ayar gaba, abunda nake nufi ga waɗanda basu ganeba shine misali idan aka rubuta ayar farko ta suratul Tauba, ana kaiwa qarshen ayar sai arubuta wannan ayar danace, bayan an rubutata sai sai a rubuta aya ta 2 ta suratul Tauba, bayan an gama rubuta aya ta biyu ta suratul Tauba ɗin a gabanta sai a rubuta wannan ayar, in angama rubuta ayar sai a rubuta aya ta uku itama a rubuta a yarda nace a rubuta a gabanta, a haka a haka har a gama rubutun surar gaba ɗaya, bayan angama rubutun an tabbatar ba kuskure sai awanke rubutun acikin qwarya kokuma a cikin kwano mai kyau mai tsarki, wanda zaiyi aiki da rubutun sai yaje yasamu wuri mai cikakken tsarki, kamar cikin ɗaki mai tsarki haka ko inda yakesa qasa mai tsarki ko tsakar gida inda ba wanda dai zai gansa, yacire kaya yayi wanka da wannan ruwan rubutun, kar yasanya kayansa sai jikinsa ya bushe duka, in an gama sai asamu quli quli ko qarago a wata hausar da siga arabawa yara a nemi biyan buqata a wurin Allah kuma a saka ido akan maqiya aga abunda zai samesu, kuma kaida suke jifa Insha Allah kafi qarfin jifa daga garesu domin ka yiwa kanka dafa'i mai qarfi.
Alhamdulillahi na saki sirrin karyq sihiri wataninda suka wuce, kuma mutane da yawa daga sassa daban daban na garuruwa daban daban da qasashe daban daban sun kirani, wasu kuma sun yimun magana a WhatsApp alhamdulillah mutane bila adadin sun amfana da wannan sirrin sunyi murna sunyi godiya, mun yiwa dubban mutane wannan aikin wallahi kuma sun samu biyan buqata sunyi farin ciki sun samu sauqi cikin iyawar Allah.

Jama'a awannan zamanin damuke ciki fa al'amura sai mun kula da maqiya da mahassada yanda zamu kauce musu kumamuyi maganinsu, kuma wallahi tallahi a zamaninnan mafi yawancinmu ana jifanmu ana yimana ture, da kambun baka, kowa yanada maqiya, saboda haka kuzo kuyi aikinmu na ya qahharu wanda muka bayar kuma kuyi wannan domin kiyaye gaba, in kunada hali kuzo ayi muku domin hakan yafi sauqi agareku, ku nememu a 08136560680 ko kuyi magana a WhatsApp.

Allah yasa mu dace duniya da lahira Allah ya tsaremu ya karemu ya kiyayemu daga dukkanin sharri da fitina da masifa, Allah yayimana jagora cikin dukkanin al'amuran rayuwar mu.

Domin neman qarin bayani kokuma masu neman muyi musu wannan aikin na karya sihiri ko dafa'i ko mallaka ko wacce take son yin aure ko maganar kasuwanci, kokuma aiki wanda yashafi al' amuransu ko lafiyarsu ko mu'amalarsu sai su tuntube ni akan numbobina ko akan WhatsApp a wadannan numbobin nawa👇
09020132884

Ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa

Alhamdulillah
Next Post Previous Post
2 Comments
 • Unknown
  Unknown July 5, 2020 at 9:51 AM

  Baihauba

  • Shehudiezer
   Shehudiezer April 10, 2021 at 3:43 AM

   Afwan,menene baihauba?

Add Comment
comment url