Maganin Mayu Mujarrabi

MAGANIN MAYU SAHIHI MUJARRABI

 Assalamu alaikum warahmatullah ta'ala wabarakaatuh, mabiya shafin shehu diezer na kullum na kowacce rana mazan ku da matan ku barkanku da wannan lokaci da fatan kuna cikin qoshin lafiya, allah ya sa haka ameen, dukkanin ku ina yi muku fatan alkhairi duniya da lahira Allah ya qaramana lafiya ya sa mu dace 

INA WANDA YAKEDA MATSALAR MAYU, KOKUMA WANDA MAYU SUKE KAI MASA HARI?
Yau wannan sirrin wannan aikin naku ne ku kaɗai.

Wanda mayu suka shi a gaba ko suka saka ɗan sa a gaba, ko mahaifi ko mahaifiyarsa, ko matar sa, ko ƴar sa, ko budurwar sa ko ƴan uwansa ko abokanan sa ko wani wanda ka sani, ko ƴar ki ko ɗan uwan ki ko wani wanda kika sani, an yita yin magani amma an gagara magance matsalar su, to ga abubuwa ko ince magunguna ko sirruka guda biyu masu sauqi waɗanda za'a jarraba a rabu da suka yi y alfarmar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama.Ana rubuta wannan Saqandamin na sama👆👆 a allo , a yanda aka ganshi a haka za'a rubuta qafa goma sha huɗu (14) a wanke abaiwa wanda yake fama da lalurar yasha ko wadda take fama da lalurar ta sha, za'a dinga rubutawa kullum har zuwa kwana 3 ko kwana 4 ana ba shi yana sha, Insha Allah in dai matsalar mayu ce to za'a rabu da ita Insha Allah za su sake shi ba tareda ɓata lokaci ba
MAGANIN MAYU 2:

Mabiya shafin shehu diezer ga wani maganin mayun zan baku, mai qarfi ne daga wani Malaminmu Halliru Jafar Shu'aibu, mujarrabi ne ya jarraba shi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba👇
Wannan maganin mayu ne ƴaƴan matsiyata, na itace ne babu rubutu ko wani wahala, sassaqen itatuwa ne za'a nemo ko za'a siyo, in an siyo ko an ebo ko an samo sassaqoqin itatuwan aka haɗa maganin to wlh duk irin kalar kamuda mayu suka yi maka sai sun sake ka da gaggawa.
Kuma wannan sirrin da zan baku dafa'in mayu ne ba maganin su kaɗai ba, kariya ne da tsari daga gare su, kai da faɗawa hannunsu wallahi har abada, mayu zasu dinga tsoron ka idan kana waje maye bai isa ya zo gurin ba wallahi, in ma yazo da sauri da gudu zai bar gurin, ba zai iya zama ba, in kuma yana wurin sai ka zo gurin to tashi zai yi ya baka wurin, ko hanya ɗaya kuka haɗa/ zaku haɗa da maye da zarar ya hangoka zai chanza hanya in akwai wani lungu zai shige ya ruga ko ya ɓace, ba zai iya zuwa ya wuce ka wuce ba, kokuma ku dinga tafiya a ɓangare ɗaya dashi, bai isa ba, ba zai taɓa iya zama inuwa ɗaya da kai ba, ka yi masa yawa, misali koda a ce maqotan gidan ku mayu ne to tashi zasu yi subar gidan domin ba zasu iya zama ba, dole ne su qaura daga anguwar ko garin gabaɗaya.

Kuma wannan maganin mayu basu isa su lalata shi ba, duk gidan da wannan maganin yake basu isa sun kusanci wannan gidan dan uban su, gidan ya fi qarfin su, kai ko ɓeran gidan ko kazar tafi qarfin maye ballantana ɗan gidan, in ka haɗa wannan maganin zaka san ka haɗa maganin mayu mai kyau yanda zaka ji yanayin tashin qamshin maganin ma zaki gane.

Ba tareda ɓata lokaci ba ga yanda ake haɗa maganin👇
Asamo waɗannan itatuwan👇
Saiwar Sanya
Saiwar chizãqi
Saiwar jema
Saiwar farar qaya 
Saiwar zogale/ zogala
Saiwar daddoya
Saiwar gwandar rafi ko sassaqen duk daya ne. 
In an samo dukkanin su sai a haɗa su waje ɗaya a jiqa su a cikin wani mazubi mai girma mai kyau mai tsafta, in aka jiqa waɗannan saiwar itatuwan suka jiqu sosai sai ku dinga sha kuna shafe jikinku kai da iyalanka ko kai da matar ka ko kai da iyayen ka ko kai da iyayen ka da yan uwan ka har ya qãre, idan ya qare a qara masa ruwa, in ya qara qarewa a qara qara masa ruwa,anayi ana qara ruwa har ya salafce yazama ya sillãce.
Insha Allah in kayi/ kikayi/ kukayi wannan aikin to kaida qara haɗuwa da sharrin mayu har abada, kai da duk wanda ya sha wannan maganin sosai har ya bi jikin sa to kun fi qarfin maye, wanda yake tare daku ma yafi qarfin maye ballantana ku. Bakuda sauran matsalar mayu Alfarmar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wa sallam

Malam yace shima kun ga nashi wanda ya jiqa yake sha duk bayan shekara ɗaya sai yayi wannan maganin saboda tsaro ba don tsoroba👇Idan ka samu wani dan uwanka ko dangin ku ko abokinka yanada matsalar mayu ko mayu suna harin sa to ka gaggauta yi masa sharin din wannan aikin, ba'a wasa da matsalar mayu, idan maye ya kama ka cikin sauqi zai iya kasheka idan aka yi wasa, a dinga daukar mataki da wuri, Allah yasa mu dace amin.

Domin tambaya kokuma domin neman qarin bayani akan wannan sai a tuntuɓemu a waɗannan numbobin 👉 08136560680 (WhatsApp and Call), kokuma 09020132884

Muna yin ko wane irin aiki na magunguna da asrarai da addu'o'i da shawarwari, game da matsalar aure ko soyayya ko firaqu mai dalili, ko kasuwanci ko takara ko siyasa ko dafa'i ko jalabi ko istihara ko Ramli da binciken rayuwa da binciken aure da gane yanda aure zai kasance duk ina yi.
Bayan haka ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
Tiktok: 
YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url