Addu'ar Neman Wata Biyan Buqata Awurin Allah (SWT)
ADDU'AR NEMAN WATA BUQATA AGURIN ALLAH (SWT)
Assalamu alaikum warahmatullahi jama'a yan'uwa mata da maza da fatan dukkaninku kuna lafiya kuma da fatan kuna biye dani acikin wannan shafin nawa mai albarka, ina godiya da hakan Allah yaqara zumunci ameen..
Ku kasance kuna bibiyar wannan shafin namu mai albarka wanda muka qyar qyareshi domin amfani da magani da warakar al'umma masoya Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam, Insha Allahu zaku samu duk wasu sirruka da magunguna da dafa'i da jalabi da duk wasu abubuwa da kuke buqata wadanda zasu yimuku amfani yau da gobe, stay tuned.
Ayau dai bayaninda na zo muku da shi zamu yi magana ne akan yadda zaka yi addu'a kokuma zakiyi addu'a ga Allah (SWT) domin Neman biyan buqatar wata buqata taka ta alkhairi, kuma domin Neman taimakon Allah acikin wani abunda kake nema amma yaci tura, kokuma yaqi cigaba yaqi yiwuwa yayi tsaye ba cigaba, kayi kayi amma yaqi daidaituwa yanda kake so, kayi duk yanda zakayi amma shuru, to Insha Allah yau sirrinda na kawo muku shine addu'a da na ciro daga cikin Alqur'ani yanda zaka roqi Allah wata buqatarka mai girma domin samun biyan buqata cikin gaggawa.
Kamar kullum dai muna gaya muku kuma kun san cewa shi Allah subhanahu wata'ala wadatacce ne mai arziqinda bashida iyaka mai kyautarda baya rowa mai mulkinda baya qarewa, Allah mai tausayin bayinsa mai afuwa da yafemusu da gafartamusu da amsa addu'o'insu, indai anyi wannan addu'ar a lokacinda akace to tabbas za'a samu biyan buqata daga Allah in Allah ya yarda.
Note: Za'a yi wannan addu'ar ne acikin sulusin dare, ma'ana tsakiyar dare daga qarfe ɗaya na dare 1:00am, zuwa qarfe huɗu 4:00am, atsakankanin wannan lokacin ne akeso ayi wannan addu'ar da wuridin domin awannan lokacin addu'a batada shamaki tsakaninta da Allah sarkin sarakuna, da zarar anyita Insha Allah ta karɓu ba shakka da yardar Allah, Allah ya tabbatar mana da cewa acikin dare alokacinda bayinsa suke barci yana saukowa sammai bakwai domin yaga bayinsa wadanda suke addu'a ya amshi addu'ar su da masu roqonsa ya amshi qoronsu, da masu neman yardarsa ya yarda dasu da masu neman gafararsa ya gafarta musu, da masu neman arziqi ya azurtasu, da masu neman tsari daga sharri ya tsaresu, da dukkanin masu wata buqata idan dai suna tashi suna neman wannan buqatar a tsakiyar dake to Allah ya tabbatar da cewa zai amsamusu, da wannan muke cewa atashi atsakanin qarfe 1 nadare zuwa qarfe 4 na asuba ayi wannan addu'ar, ga yanda addu'ar take👇
Da farko dai za'a saka kaya mai kyau, inson samune asaka fararen kaya, maza da mata kowa zai iya yin wannan addu'ar, maza zasu iya daka farar jallabiya ko farin yadi ko farar shadda mai riga da wando da sauransu, mata kuma zasu iya saka farin hijabi dogo ko fararen kaya.
Bayan ansaka fararen kaya sannan sai ayi alwala, sannan ayi niyyar yin wannan addu'a, sannan asamu Alqur'aninda zaka iya karantawa HAFSU ko WARSHU sannan abuɗe Alqur'anin abuɗo suratul HUUD, Surah ta goma sha ɗaya (11) daga fatiha, bayan anbuɗo suratul HUUD sai aduba aya ta shida (6), a farkon izu, za'a ga ayar kamar haka👇
“Wamã min dãbbatin fil ardi illa alallahi rizquha wa ya'alamu mustaqarraha wa mustau da'aha kullun fii kitabin mubeen”
Idan anga wannan ayar sai ayi shaida awurin ko asaka wani abu tayanda koda an rufe shafin za'a iya qara buɗo wannan shafin cikin sauqi, idan anrufe an ajiye Qur'anin a gaban sallaya ko tabarmarda za'ayi wuridin akai, sai ayi nafila raka'a hudu (4), Istigfari qafa ɗari (100), Salatin Annabi qafa ɗari (100), La ilaha illallahu qafa ɗari (100), bayan angama sai akaranta wannan ayar dana faɗa ta sama qafa dubu ɗaya (1000) cif.
Bayan angama wuridin wannan ayar sai aroqi buqata awajen Allah subhanahu wata'ala, sannan sai ayi sadaqa da abunda ya sauwaka, (qosai, ko masa, ko kudi,) e.t.c, Insha Allahu zaka samu biyan buqata acikin lokaci qalilan, wannan sirrin mujarrabi ne, wannan ayar aya ce mai falala, tana bayani ne gameda girman Allah da izzar Allah da arziqin Allah da rahamar Allah.
Yan'uwa Dan Allah ayi qoqari ayi wannan addu'ar domin tanada ijaba sosai kuma sannan tanada amfani sosai,
Domin neman qarin bayani kokuma masu neman ayimusu wani aiki na karya sihiri ko mallaka ko wacce takeson yin aure ko maganar kasuwancinku ko aiki wanda ya shafi rayuwarsu ta yau da kullum kokuma lafiyarku ko mu'amalarku sai su tuntubeni akan numbobin wayata kokuma akan WhatsApp a wadannan numbobin👇
08136560680
09020132884
Duk Wanda yakeda tambaya sai yayi comment da tambayarsa kokuma yakirani awaya 08136560680, Allah yasa mudace duniya da lahira ameen.
Kuma Insha Allahu darasinmu a nan gaba kaɗan in kuna bibiye damu zamu nuna muku yadda ake yin ISTIHARA, domin istihara tanada matuqar amfani, kuma sunna ce domin komai annabi (SAW) zai yi sai yayi ISTIHARA YAGANI AKWAI ALKHAIRI KO BABU,
Allah yasa mudace, ameen.
Subhana rabbika rabbil izzati amma yasifuun
Wa salaamun alal mursalin
Walhamdu lillahi rabbil alameen
shehudiezer.com
Yayi kyau Allah yasa alkhairi
Mashallah
Mashaalllahu
Alhamdulillah
Mashallah