Sirrin Hana Zina Da Fasiqanci

SIRRIN HANA ZINA DA ALFASHA 

Asssalamu alaikum wa rahmatullah ta'ala wa barakatuhu jama'a maza da mata, ina yi muku fatan alkhairi, Allah ya sa mu haɗu musha madara a aljanna a gaban shugaban halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam amin, Allah ubangiji ka yimana muwafaqa a addini, Allah kar ka bari son zuciyarmu ya halakar damu, kuma ya Allah kada ka bari shaiɗan la'ananne ya durmuyar da mu ya ɗoramu akan hanyar halaka amin, Allah kasa mu yi kyakkyawan qarshe.
Kamar yanda na saba, yau na zo muku da sirri mai matuqar amfani mai matuqar muhimmanci a cikin al'ummar mu ta musulmi, sirrin hakan zina da kuma dakatar da wanda yake yi, kamar yanda kowa ya sani zina ta zama ruwan dare, alfasha ta shiga ko ina, zina ta bazu a cikin al'ummar musulmi wal'iyazu billah, duk girman mutum duk musuluncin sa duk imanin sa duk tsufan sa duk yarintar sa duk keɓancewar sa duk ilimin addinin sa duk tsoron Allan sa wallahi a wannan zamanin sai wanda Allah ya tsare daga wannan musibar, maza zina, mata zina, iyaye zina, ƴaƴa zina, matan aure na sunnah zina, gwauraye mara aure zina malamai zina, yara zina, ma'aikata zina, ƴan kasuwa zina, ƴan siyasa zina, yaran gida zina, masu talla zina, ƴan makaranta zina, ɗalibai zina, tsofaffi zina, samari zina, ƴan mata zina, waɗanda aka saka musu ranar aure zina, namiji mai aure zina, zina ta shiga al'umma har inda hankali bazai ɗauka ba yanzu zina shiga take yi, ana samun case ɗin zina a tsakanin matar uba da ɗa, ana samun case ɗin zina a tsakanin yaya da qanwa, maqota da maqota, tsakanin cousins, zina a tsakanin masu neman aiki da masu bayar da aiki (employers), a tsakanin malamai da ɗalibai ana yin zina domin cin jarabawa ko domin passing jarabawa a makaranta, har tsakanin uba da ƴa ko uwa da ɗa innalillahi wa inna ilaihi raji'un, har a tsakanin qanen miji da matar yayan sa, kokuma mijinki ya dinga kwanciya da qannen ki idan sun zo gidan ki ko suna zaune a gidan ki, har suyi soyayya har ya lalatata baki san ana yi ba, don rashin haquri da lalacewa da jarrabawa wasu ma an saka musu ranar aure amma a haka suke yin zina, wani kuma a ranar auren sa ma sai yayi zina ko ana washe gari auren sa, wani kuma bayan ya yi aure zai cigaba da kasancewa da matan banza fiye da matar sa ta sunnah, wallahi cases na zina da fasiqanci sunanan da yawa, duk yawan rubutuna duk yawan tunanin mutum bazai taɓa iya zayyano dukkanin cases na zina da suke faruwa a zamaninnan ba, kawai sai dai mu ce Allah ya kiyaye mu Allah ya shiryar da mu.
Ba tare da ɓata lokaci ba, ga sirrin, idan mace tana Zina kokuma namiji yana zina an tabbatar da haka, to ga aikin da za'a yi alfarmar Annabi da Alqur'ani ko wanene zai daina kuma ko wacece zata dainaZa'a rubuta wannan hatimin na sama qafa saba'in da uku (73), a wanke sai a nemo qasar masallaci wanda yake tara jama'a a barbaɗa a cikin rubutun a bata / a bashi yasha, in kuma so samu ne ayi kamar sau 3 ko bakwai.
 Insha Allah zata /zai daina yin zina.

Kokuma a nemi wannan hakin (ganyen) wanda kuke ganin hoton sa a nan qasa👇

Kafin ka taɓashi

Bayan kã taɓashi


mu dai a hausar garin mu muna kiran sa da suna 
RUFE WALKINKA wasu kuma suna ce masa TATTARA KAYANKA, kokuma RUFE RUMBU ko TAƁA RUMBU, in an tambaya wurin ƴan ganye masu siyar da itatuwa da ganyen gargajiya a kasuwa za'a sameshi.
Amma yanda hakin yake shine:- zaka gan shi kunnuwan sa a buɗe amma kana taɓa shi da hannu zaka ga ya ɗago kunnuwan sa gaba ɗaya ya rufe saman sa da kansa, kamar dai yanda kuka gan shi a hoton chan na sama, kuma idan ya rufe kunnuwan sa zai ɗauki lokaci mai tsayi bai buɗe ba.
To idan aka siyo / aka samo wannan haki sai aɗebo shi da ɗan yawa, sai a daka shi sosai, a shanya shi, idan ya bushe sai a sake daka shi a tankaɗe shi, sai a nemi allo da tawada sai a rubuta “Bismillahirrahmanirraheem” qafa bakwai (7), sai a rubuta “Ihdinassirãɗal mustaqeem” qafa ɗaya tak (1), sai a rubuta “qããla ma'ãzallãh” qafa bakwai (7), sai a rubuta “walã taqrabuzzinã innahuu kãna fãhishatan wasãã'a sabiilã” qafa bakwai (7), dukkanin su da larabci za'a rubuta si.
In an gama rubutawa gaba ɗaya sai a wanke rubutun gaba ɗaya a haɗa shi a wuri ɗaya, sai a saka hannu a damqi garin wannan hakin da aka tankaɗe kaɗan a saka a cikin rubutun asha, gobe ma a sake rubutawa kamar yanda aka yi a baya the same, a saka garin maganin a baiwa mai fama da matsalar yasha / tasha, kullum haka za'a yita yi har tsawon kwana bakwai (7).
To in dai an gama wannan aikin kuma an tabbatar mai fama da matsalar ya sha to Insha Allahu ba dai zina ba, zai daina zai watsar da zina zata fita a ransa zata daina dawowa a ransa, wallahi ko karuwa aka yiwa wannan aikin to zata rabu da zina bazata sake karuwanci ba da izinin Allah
Sirri ne mujarrabi, an gwada yayi aiki.
Allah yasa mu dace, Allah ya bada ikon yi, kuma Allah yashiryar da Al'ummar musulmi baki ɗaya.
Domin neman qarin bayani ko waɗanda suke da tambaya ko neman bayani gameda wani sirri ko laqani da na saki ko wadanda suke so a yimusu wannan aikin kokuma wani aiki kokuma a magance musu wata matsala tasu da yardar Allah da ikon Allah zasu iya yin comment a qasa kokuma zasu iya tuntuɓarmu a numbobinmu kamar haka👇👇
08136560680 (WhatsApp shehudiezer)
09020132884 (available)
Bayan haka muna sanar da ƴan uwa cewa muna yin aiki domin matsalar ku, aiki ko wane iri ne in dai bai saɓawa Allah da Annabin rahama ba, to muna yi, misali in aiki ne na magunguna da asrarai da addu'o'i da shawarwari duka, duk wanda yake da buqata game da matsalar sa ko wace iri ce in dai ta duniya ce, insha Allahu a tuntuɓeni za'a samu dacewa da izinin Allah
Next Post Previous Post
1 Comments
  • Anonymous
    Anonymous August 26, 2022 at 1:24 AM

    جزکم اللہ خیرا

Add Comment
comment url