Maganin Sata Da Mayarda Abunda Aka Sata

SIRRIN MAYARDA ABUNDA AKA SATA MUJARRABUN
Assalamu alaikum wa rahmatullah ta'ala wabarakaatuh jama'a ƴan uwa masoya Manzon Allah Sallallahu alaihi Wa sallama da fatan kun wuni lafiya kuma kuna cikin cikakkiyar lafiya, Allah ya sa haka amin summa amin

Allah ya qara tsira da yabo ga Annabi Muhammadu Shugabanmu SAW da iyalansa da sahabbansa da sauran bayin Allah salihai da tabi'ai da mursalai da dukkanin waɗanda suka biyo bayan sa da ihsani har zuwa ranar tashin alqiyama 

Kamar kullum kamar kowane lokaci, yau na zo muku da wani sirruka ɗaya zuwa biyu Mujarrabai ne an gwada su sun yi aiki Insha Allah, sanadiyyar sace sace da yayi yawa a ƴan kwanakinnan a cikin kasuwanninmu da shagunanmu da wuraren sana'armu da gidajenmu da ɗakunanmu da hanyoyinmu sa sauransu, qasa ta lalace talauci da rashin tsaro ya yawaita saidai muce Allah yayi mana maganin wannan abubuwan.

Wannan sirruka guda biyu ne zan ba ku, a cikin su ko wanne aka yi aiki dashi za'a dace kuma za'a samu biyan buqata da yardar Allah, ga yanda aikin yake👇

Wannan aikin ana so a yi shi ne a ranar da aka sace abun kokuma a ranarda aka nemi abun aka rasa, kokuma misali idan kun kwanta barci kuka tashi da safe kuka ga an yimuku sata kokuma an ɗauke muku wani abu ko ɓarayi sun diro sun shigo gidanku ko ɗakinku sun saci wani abu, to a ranarda aka nemi abun aka rasa kokuma a lokacinda aka ga cewa an sace wani abu a lokacin ake so ayi wannan wuridin.
Wallahi tallahi ni shehudiezer dakaina na gwada wannan aikin a kwanakinnan ma a ranar 22nd June, 2023 ɓarawo
 ya satar mun pannel na solar a sabuwar anguwarda muka koma, banma san wanda zan tambaya ba ko wanda zan baiwa cigiya a anguwar, amma cikin ikon Allah wallahil azeemu saida asirinsa ya tonu, wasu yara da ban sansuba suka zo suka ce an ga pannel a hannun wani, labari yanata yawo a anguwa har labari ya zo baki wata yarinya wacce take zaune a gidanda muke, daganan ta sanar dani, addu'a kenan, har yayi kwana 5 da siyarda pannel din har wurin wanda ya siyarwa da pannel ɗin saida mukaje amma kuma cikin ikon Allah pannel dina ya dawo hannuna, ga hoton pannel ɗin har alamun inda ya tsinke igiyar pannel ɗin ya gudu dashi zaku gani nayi alama, bayan na karɓi kayana ne na gyara wurin👇Abunda yasa na baku wannan labarin saboda kusan cewa addu'o'i daga cikin Alqur'ani da sunnah gaskiya ne, domin wannan sirrin mai rai ne kuma mujarrabi ne akaina, kuma aya ce daga Alqur'ani, wallahi mafi yawancin abubuwanda nake ɗorawa a wannan shafin na gwada su sun yi amfani ne shiyasa nake tura muku kuma ku amfana, aikin ba wani aiki ne mai wahala ba wallahi wuridi ne a awa ɗaya zaku iya gamawa, domin ni ban ma yi awa ina yinsa ba nagama, batareda ɓata lokaci ba ga aikin👇
Dazarar ka duba abunka kaga baka ganshi ba an sace shi kokuma aka yi maka sata to kayi alwala ka tabbatar kana da tsarki, bayan kayi alwala sai ka zauna akan carpet ko tabarma ko wuri nai tsarki, sai kayi Istigfari qafa ɗari (100) da Salatin Annabi qafa ɗari (100) da La ilaha illallahu qafa ɗari (100), sai kafara wuridin wannan ayar👇
“Yã bunayya innahãã intaku misqããla habbatin min khardalin fatakun fee sakhratin au fissamãwãti au fil'ardi ya'ti bihallãh innallaha laɗeefun khabeer” qafa dubu ɗaya da wani abu, ma'ana dai ana so wuridin yafi qafa dubu ɗaya koda kuwa dubu ɗaya da qwara ɗaya ne (1001) ko dubu daya da guda ashirin (1020) ko dubu ɗaya da guda hamsin misali, koma nawa ne anaso dai yafi dubu ɗaya, kar ayi wuridin qasa da dubu ɗaya, in an gama wuridin ayi addu'a akan Allah ya mayarmaka da abunda aka satarmaka alfarmar Annabi Muhammadu, magana ta qare, kajira dawowar kayan ka kawai da yardar Allah, ku gwada ku sha labari.
La shakka fihi.

SIRRI NA BIYU👇

In aka sace muku wani abu ko yaɓata a samo ko a nemo ganyen tumfafiya guda bakwai (7), kowane ɗaya a rubuta “summa Inna alainã bayããnahu” qafa ɗaya (1) a buɗe mi'ara (mimun) da hakuri (Hã'un), bayan an rubuta to a cikin Ha'un ɗin bayããnahu ɗin za'a saka sunan abunda ba'a ganiba kokuma abunda aka sace.
Bayan an rubuta sunan sai a samu guntun gawayi madaidaitu guda 7 aje bayan gari a haqa rame dai dai gwuiwar hannun ka, sai kafara saka ganyen, in kasaka ganye guda ɗaya sai kasaka gawayi guda ɗaya, sai kabi bayansa da ganye na biyu sai ka saka gawayi na biyu, sai abi bayan gawayin da ganye na uku sai aɗora gawayi na uku akan ganyen na uku, a haka a haka za'a yita yi har ganyen da gawayin su qare, in sun qare sai ka rufe ramin da ka saka ganyayen tumfafiyar da gawayin da qasa.

To Insha Allah in dai an yi aikin dai dai yanda yake ba'a samu ruɗani ko kuskure ba, to insha allah sai abin ya bayyana kokuma asirin ɓarawon ya tonu.
Wannan sirri ne mujarrabi sahihi, Allah ya rabamu da ɓarayi masu neman talauta al'umma tareda sace kayan al'umma, Allah ya wadatar damu ya bamu arziqi mara yankewa mai amfani, da lafiya cikakkiya.
 
Wanda yake da tambaya kokuma yake neman qarin bayani akan wannan sirrin ko wasu daga cikin sirruka na sai yayi comment a qasa kokuma yamun magana a WhatsApp ko ya kirani a wannan numbar tawa 08136560680, 09020132884 
Mai buqata a yimasa wannan aikin ko wani aiki daban zai iya tuntuɓarmu 
Bayan haka ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
Tiktok: 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url