Maganin Kasuwa Da Samun Cinikayya

MAGANIN KASUWA DA DAFA'IN WURIN SANA'A SAHIHI MAI INGANCI




Assalamu alaikum warahmatullah ta'ala wa barakaatuhu, was salatu was salamu alã sayyiduna Muhammadun sayyidil awwalina wal ãkhireen wa imamul mursaleen.
 Amma ba'ad, ƴan uwana maza da mata masu albarka kamar kullum dai na saba kawo muku sirruka da magunguna da laqani mujarrabun masu kyau da inganci, hausawa sun ce kasuwanci sai da kudi kuma sai da kulawa, ba mai shiga filin daga sai wanda ya shirya, to ga wata fa'ida yau kuma na kawo ta musamman ga ƴan uwan mu ƴan kasuwa waɗanda suke kokawa akan rashin jama'a da rashin samun ciniki a wurin kasuwanci da matsalolin taɓarɓarewa kasuwanci da tarin maqiya da mahassada a cikin kasuwanci kokuma a wurin kasuwanci, to wannan aikin naku ne ku saurara kuma ku mayarda hankali sosai, duk wanda matsala irin wannan ta shafa to ya kwantarda hankalinsa ga sirri musamman domin ku👇

Aikine na simiyya mai sauqi ne sosai ga wanda yake iya haɗawa.
Na samo wannan babban sirri ne daga hannu / bakin babbam malaminnan na duniyar asraru da duniyar taurari da falakiyya wato Sheikh Ibrahim Kumbu, Allah ya qara shiga lamuransa a duniya da kuma lahira amin.

Ga yanda aikin yake, a kula sosai saboda wannan aikin aiki ne na simiyya inji Shehu, aiki ne mai ɗimautarwa mai kulle kai, amma idan an nutsu za'a gane kuma za'a iya haɗashi lafiya qalau bawata matsala da yardar Allah , ga aikin👇
Abubuwanda ake buqata wurin yin wannan aikin sune👇
1- Farin qyalle
2- Ƴaƴan dabino ko ince qwallon dabino guda bakwai (7)
3- Alkama, kamar cikin hannu ɗaya
4- Ƴaƴan lalle
5- Kanumfari
6- Hulba
7- Kwalba, ƴar madaidaiciya
8- Qasar gidan yanyawa
9- Diddigen qafafuwan zomo (Heel of rabbit)

A samu ƙwallon dabino ( ƴaƴan dabino) guda bakwai masu kyau a wanke su, bayan an wankesu a ɗan shanya su, bayan an shanya su sun bushe sai a rubuta kowani harafi daga cikin waɗannan haruffan ( Fa'un, Qafun, Jimun, Mimun, Khã'un, Mimun, Tã'un) a kowane ƙwalli ɗaya, ma'ana ko wanne harafi guda ɗaya yanada qwallon dabino ɗaya (1), misali idan an ɗauki qwallon dabino ɗaya na farko sai a rubutamasa harafin Fã (Fa'un), sai in ajiyeshi a gefe sai in ɗauko wani qwallon daban in rubuta masa harafi na biyu harafin Qaf (Qafun), shima bayan an rubuta masa harafi na biyu sai a ajiyeshi a gefe, sai a qara ɗauko qwallon dabino na uku acikin guda bakwai da aka samo aka wanke, sai a rubuta masa harafi na uku harafin Jeem (Jimun), shima sai a ajiyeshi a gefe, a haka a haka za'a bisu ɗaya bayan ɗaya a rubutamusu harafi ɗaya ɗaya su bakwai ɗin, kowanne qwallon dabino ɗaya zai samu harafi ɗaya, bayan an rubutawa kowane qwallon dabino ɗaya harafinsa sai a haɗa ƴaƴan dabinon ko ince qwallayen dabinon a ɗaure su a cikin farin ƙyalle tare da wannan alkamar da ƴaƴan lalle da ƙaranful da hulba da aka samo ko aka siyo, sai a sakasu a cikin kwalbar.

Sai azo a zuba ƙasar gidan tururuwa tare da ƙasar gidan yanyawa a cikin kwalbar, tare da diddigen ƙafafun zomo (heel of rabbit 🐇) gaba ɗaya a haɗa su asakasu a cikin kwalbar sai a binne kwalbar a wurinda ake sana'a ko wurin kasuwanci, misali idan kana da rumfa ne a kasuwa sai ka binne kwalbar a cikin rumfarka, idan kanada shago ne sai ka binne kwalbar a shagonka, idan haya kake yi a shago sai ka fasa inda kasan zaka iya gyarawa a cikin shagon ka binne kwalbar, idan a gida kake kasuwancinka sai ka binne a gida, idan a mota kake kasuwancinka sai ka ɓoye kwalbar acikin motar, idan a baro ne sai ka ɓoye kwalbar a baron, koma a ina ne sai ka binne ko ka ɓoye kwalbar a wurin insha Allah.

In dai an yi hakan cikin nustuwa an gabatarda aikin cikin kamala kuma an yi komai yanda aka faɗa to customers da jama'a ƴan cinikayya ba zasu taɓa yankewa a wurin ba, hakama sihirin aljanu da mutane duk hassadar su ba zai taɓa fuskanto wurin sana'ar ka ba, saboda albarkacin duddugen zomon da yake a ciki.

Kar a manta ga harrufan da za'a rubuta a jikin qwallayen dabinon👇
ف ق ج م خ م ت
Wannan sirri ne daga Taskar malam abun alfaharinmu a duniyar asraru da kimiyya da siymiyya Sheikh Ibrahim Kumbu (RTA) Allah ya saka masa da alkhairi ya biya masa buqatunsa na alkhairi ya qaramasa lafiya yasa ya gama da duniya lafiya amin.
Masu tambaya zasu iya kira kokuma suyi tambayar a comments section
Alhamdulilllah.
Domin waɗanda suke so a yimusu wannan sirrin kokuma a haɗamusu a aikamusu a garuruwanda suke, ko wadanda suke son ayimasu wasu ayyuka daban ko suke neman shawara ko bayani sai su kira a waya kokuma su yimun magana a WhatsApp 08136560680, 09020132884
In ankira ba'a samuba to za'a sameni a ɗayar numbar ta zain 09020132884 kokuma a WhatsApp 08136560680

Alhamdulilllah
Sannan bayan haka ina mai yi muku albishir insha Allah nan gaba zan yi bayani game da gidajen aure da bayanan sharikar aure da bayanai game da ɗabi'u da burujai domin sauqaqa lamurran zamantakewar aure da matsalolin sake sake da rabuwa da faɗa da rashin jituwa da muke fama da su a auratayyar mu, zamu yi bayani gameda irin namijinda ya kamata mace ta aura dakuma irin matarda ya dace namiji ya aura duka insha Allah, ku kasance tare da mu

Bayan haka ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
Tiktok: 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url