Lokutanda Ba'a Saduwa Da Iyali

LOKUTANDA BA'A JIMA'I DOMIN  YAKAN IYA CUTARDA MA'AURATA KO ƳAƳANDA ZASU HAIFA KO ZURI'ARSU 


Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakãtuhu mabiya shafin shehu diezer yauma dai nine na kawomuku wasu muhimman bayanai ga ma'aurata wadanda sukeda aure kuma basuda cikakken ilimi akan rayuwar aure kokuma ince ilimi akan saduwa da lokutanda Annabi ya haramta saduwa da lokutanda ya hana a kusanci mata da sauransu, domin gujewa haihuwar ƴaƴa wadanda basuda mutunci basuda imani mara jin magana, kokuma gudun haihuwar yara mara hankali ko masu taɓin hankali kokuma gudun haihuwar yaro da wata lalura daban. Wannan dai compilation ne na lokutanda Annabi Muhammad SAW ya ja hankalin ma'aurata da su guji saduwa a waɗannan lokutan saboda hakan zai iya janyo illa garesu kokuma abunda zasu haifa.





JIMA'I LOKACIN AL'ADA: Bayan kasancewarsa haramun a Musulunci kuma yin hakan yana haifarda cututtuka munana, da ciwon hauka da mayar da ɗanda aka haifs zabaya, yana kawo cututtuka ga ma'aurata musamman ma ga mata inda likitoci suka tabbatarda cewa yana haifarda zubar jini sosai dakuma raunuka a gaban mace kamar quraje da sauransu yana kuma saka mace ta kaamu da buɗewar baakin mahaifa. 

JIMA'I LOKACIN DA MACE TAKE DA CIKI: Idan matar mai ciki ce anfi so namiji yayi jima'in cikin laushi da bi ahankali cikin lumana don kaucewa matsalolinda ke janyo ƁARI tare da kiyaye irin yanayin kwanciyarda ta dace da mai cikin idan kuwa cikin yaa kai wata takwas to yakamata maigida ya haqura da jima'in har sai ta haihu. 

JIMA'I BAYAN HAIHUWA KO BARI: Bayan mace ta haihu ko tayi Ɓari lallai gabanta da bakin mahaifarta duk sun wahala sunada bukatar hutu aqalla sati biyu zuwa sati uku har zuwa wata ɗaya don kaucewa kamuwa da matsaloli. 

JIMA'I GA MA'AURATANDA KE DAUKE DA CUTAR SANYI KO INFECTION: Kuskurene babba ga duk ma'auratanda sukeda infection su dinga kusantar junansu sbd duk matarda takeda sanyi ko toilet infection bazata warke ba matukar ana jima'i da ita kuma cutar zata daɗa samun gurbin zama a jikinta, don haka ma'aurata su hakura da juna sai an warke

Ga bayanan Annabi Muhammad SAW acikin hadisai gameda lokutanda ba'a saduwa da iyali:
Acikin hadisi Annabi Muhammad (saw) ya ke cewa Sayyiduna Ali (as) da ya koyar da mutane wannan abin da zaizo : “ya ali ka da ka jewa matarka a farkon wata ko tsakiyarsa da karshensa, lalle hauka da kuturta da rauni na gaggawa gareta da danta”

“Ya Ali , duk wanda ya kasance cikin janaba a shimfida tare da matarsa kada ya karanta Qur'ani, hakika ni ina jiye musu tsoron kada wuta ta sauko daga sama ta konesu”.

“Ya Ali , ka da ka je ma matarka a cikin sha'awar matar waninka, lalle ni ina jin tsoron idan ubangiji ya hukunta da tsakininku zai kasance mata maza, mai karkata ya zuwa mata mai matsalar hankali”

“Ya Ali , ka da ka yi surutu yayin saduwarka da iyali, lalle al'amarin yanda ya ke shi ne idan Allah ya kaddara samun ɗa a tsakaninku ba zai aminta daga kasancewa bebe ba, ka da mutum ya dinga kallon farjin yayin jima'i matarsa, ya damke idon sa ayayin jima'i, lalle kallon farji na gadar da makanta ga yaron da za'a Haifa”

“Ya Ali , ka da ka jewa iyalinka face kaa kasance tare da kqyalle sannan suma iyalinka da qyalle, ka da ku shafi juna da kyalle guda sai sha'awa tayi karo da sha'awa, lalle hakan na janyo qiyayya a tsakaninku, sannan ya kai ku ga saki da rabuwa da juna”

“Ya Ali , ka da ka jewa iyalinka a tsaye haqiqa hakan na daga ɗabi'ar jaki, idan an qaddara ɗa a tsakaninku zai kasance mai yawan fitsarin kwance kamar jaki mai yawan fitsari a dukkanin wajen da ya samu”

“Yã Ali , ka da ka jewa iyalinka daren Eidil Fitr, lalle idan an qaddara ɗa a tsaninku zai kasance mai yawan sharri”

“Ya Ali , ka da ka jewa iyalinka a daren idin babbar sallah, lalle idan an qaddara ɗa a tsakaninku zai kasance mai yatsu shida ko hudu”

“Ya Ali, ka da ka jewa iyalinka a farkon dare, hakika idan ubangiji ya qaddara ɗa da a tsakaninku bazai aminta daga kasancewa boka ma'abocin sihiri mai fifita duniya kan lahira ba”

 “Ya Ali, ka da ka jewa iyalinka qarqashin bishiya mai ƴaƴa, lallai idan Allah ya qaddara ɗa a tsakaninku zai kasance mai kisa ko boka matsafi”

“Ya Ali, ka da ka je wa iyalinka tsakanin kiran sallah da ikama, idan Allah ya qaddarta ɗa a tsakaninku ɗan zai kasance mai kwaɗayin zubar da jini”

“Ya Ali, idan matarka ta ɗauki ciki, ka da ka je mata face ka na cikin alwala, haqiqa idan Allah ya qaddara ɗa a tsakaninku zai kasance mai makauniyar zuciya, marowaci”



“Ya Ali, ka da ka jewa iyalinka daren nisfu sha'aban, hakika idan Allah ya kaddara da tsakaninku zai zama mummuna mai tawadar Allah cikin gashi da fuska”

 “Ya Ali, ka da ka jewa iyalinka a cikin kwanaki biyun qarshen wata, haqiqa idan Allah ya qaddara ɗa a tsakaninku, zai kasance maha'inci ko mai taimakon azzalumai, sannan mutane masu yawa su halaka ta hannunsa”

“Ya Ali, ka da ka zaqewa iyalinka kan rufin gida, hakika in Allah ya kaddara ɗa a tsakaninku zai kasance munafiki ɗan bidi'a ma'abocin riya”

“Ya Ali, idan ka fito tafiya to kada ka jewa iyalinka wannan dare, hakika idan Allah ya ƙaddara ɗa a tsakaninku to zai dinga bayar da dukiyarsa cikin tafarkin ɓata” sai Annabi ya karanta wata aya, fassarar ayar itace “Lallai masu almubazzaranci sun kasance ƴan uwan shaidanu ne”

“Ya Ali, ka da ka jewa iyalinka idan ka fito tafiyar kwanaki uku da dare uku, hakika idan Allah ya qaddara ɗa a tsakaninku zai kasance mai taimakon azzalumai”

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce: “Makruhi ne mutum ya je ma iyalinsa bayan yayi mafarki yana cikin janabar mafarkin face ya yi wanka, idan kuma ya qi yin hakan ya zaqe to idan ɗansa ya fito mara hankali kada ya zargi kowa face kansa”

Annabi SAW yace: “duk wanda ya zaqewa matarsa halin ta na haila sai ɗanda suka haifa ya zo kuturu ko mai ciwon kuturta, to kada ya zargi kowa face kansa”

Manzon Allah SAW yace: “idan ɗayanku ya yi nufin jewa iyalansa to yaguji farkon wata da tsakiyarsa, haqiqa shaiɗan yana neman wanda zai yi tarayya da shi cikin ɗigon maniyyinsa a wadannan lokuta, shaidanu na neman abokanan tarayya cikinsu suna zuwa su dana tarko”

Sarkin muminai Sayyadina Ali (as) yace : “idan ɗayanku ya nufi zaqewa matarsa to kada yayi mata gaggawa, saboda tabbas suma mata suna da tasu buqatar, idan wani ya ga wata mace na burge shi to ya je wurin iyalinsa haqiqa iyalinsa na da irin abin da ya gani agurin wata, kada ya baiwa shaiɗan muhalli a cikin zuciyarsa, ya kauda idonsa daga matar da ba ta sa ba, idan bai da mata to yayi sallah raka'a biyu ya yawaita godiya ga Allah da salati ga Annabi da iyalansa (as) sannan ya roki Allah daga falalarsa, hakika Allah zai halasta masa abin da zai wadace shi, idan ɗayanku ya je ma iyalansa to ya qaranta yin surutu, haqiqa surutu yayin saduwa da iyali na gadar da bebanta, sannan kada ya dinga kallon cikin farjin matarsa ta yiwu ya ga abin da baya so kuma yin hakan ya na gadar da makanta”

Wadannan kaɗan daga cikin lokutanda Annabi Muhammad SAW ya haramta yin jima'i da matarka ne kuma ya ja hankalin masu aure da su guji wadannan lokutan kuma suyi hattara

Saboda haka jama'a ma'aurata dan allah akiyaye, idan Allah yasa ke matar aurece kikaci karo sa wannan posting din kuma kinsan kunayin kuskure kuna saduwa a waɗannan lokutan dakuma abubuwanda aka garamta a yayin saduwa kuma kinsan mijinki bai saniba yanada kyau kiyi copying link din post din ki turamasa kokuma kinunamasa yagani, saboda gobeku data ƴaƴanku tayi kyau gabaɗaya, Allah yasa mudace, daga naku shehudiezer 



Shehu diezer

08136560680 call and WhatsApp
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url