Sirrin Karya Sihiri Mujarrabun (III)

SIRRIN KARYA SIHIRI MUJARRABUN


Assalamu alaikum wa rahmatul lahi ta'ala wabarakatuh jama'a ƴan uwa musulmai al'ummar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wa sallam, ina gaishe ku tare da yi muku fatan alkhairi a rayuwa, Allah ya sa mu gama da duniya lafiya, Allah ya sa kar mu faɗa a halaka, Allah ya bamu lafiya da hankali da haquri, Allah yasa Annabi SAW ya cece mu amin.

Ni fa kun san ni da Sihiri ba shiri, ni da jifa ko makaru bama shiri, na tsani Sihiri da masu yinsa domin hassada ba gaira babu dalili, na tsani in ji wani ya ce an yi masa Sihiri ko an jefe sa, shi yasa ko da yaushe kullun a kowane lokaci bana rabuwa da manyan sirruka na karya sihiri da warwaye duk wani sharri da asiri, ba tare da ɓata lokaci ba yau na zo muku da wani gagaruman Sirrukan karya sihiri guda biyu mujarrabai, an gwada su an samu biyan buqata, a yi qoqari a samu damar aikatawa Insha Allahu za'a dace kuma za'a yi farin ciki sosai kuma za'a warware za'a samu lafiya alfarmar Annabi da Alqur'ani, ga na farkon 👇

Da farko za'a samu ganyen magarya, ga hotonta nan a qasa👇



Wannan shi ne ganyen magarya

Bayan an samu ko an nemo ganyen magarya dai dai gwargwadon wanda ya samu, ko mai yawa ko ɗan kaɗan ko ɗan madaidaici, dai dai gwargwado, sai a siyo/ a nemo Kainuwa dashen Allah, in an samo waɗannan ganyayyakin sai a shanya su su bushe sai a daka su, in kuma busasshi ne sai a daka su kawai, busasshi ma suna yi, da su da ɗanyu duk ɗaya suke.

Bayan an daka su sosai sun daku an tankaɗe su sai a dinga ibar wannan garin maganin ana zubawa a cikin ruwa a kofi ko a kwano, bayan an zuba sai a tofa Ayatul Kursiyyu qafa saba'in (70), Li'ilafi quraish har zuwa qarshen surah qafa saba'in 70, Qul a'uzu bi rabbil Falaqi har zuwa qarshen surar qafa saba'in (70) da Qul a'uzu birabbin Nasi har zuwa qarshen surah qafa 70 qafa saba'in saba'in, amma tofawa za'a dinga yi a cikin wannan ruwan rubutun mai garin maganin, in an gama tofawa a baiwa mai fama da sihirin ko asirin ko makarun ya sha/ ta sha, ko da kuwa ya kasance a kwance yake baya iya tafiya to a dinga yi masa wannan aikin, Insha Allah in dai sihiri ne ko makaru ko jifa a jikin sa zai warware, wannam aikin mujarrabun ne, yana aiki sosai, za'a samu waraka cikin yardar Allah, Allah yasa a dace, ana iya yiwa mace da namiji, yaro da babba.

Kokuma ga wani maganin karya sihiri ko jifa ko makaru ko wanne kala ko ya kai shekara nawa a jikin ka zai lalace da yardar Allah kuma dafa'i ne tsarin jiki ne kariya ne wallahi, duk malantar mutum, duk bokancin mutum koda kuwa a saman ruwa yake shinfiɗa buzun sa yake lazimi don yajefe ka wllh sai ya barka da yar dar Allah, wannan aikin ba na wasa bane, bana bayar da aikin wasa.

 Yanda ake yin sa shine ana rubuta “Wa raddallahul lazina kafaru bigaizihim lam yanããluu khairaa wakafal lahul mu'umininal qitããl wa kããnal lahu qawiyyan azeeza” da larabci qafa dubu ɗaya (1000), bayan an rubuta sai a wanke rubutun da ruwa mai kyau a sha Insha Allahu duk sihirinda yake jikin ka zai warware zai wargaje kuma zai tsare ka daga sharrin masheranta da masu jifa.

Kokuma idan sihirin da aka yi maka an haɗashi da iska ne ko aljani ko rauhani to ga aikin da zaka yi👇

Idan aka yi maka sihiri wanda aka haɗa da Aljannu kayi kayi ka karya sihirin ya qi karyuwa to in dai ka yi amfani da wannan hayaqin to indai sihirin zai karye to a lokacin da kayi wannan hayaqin da zamu bada zaka ji kasala ta rufe ka, to idan ka ji haka kar ka damu sihirin ne zai lalace da yardae Allah, yanda ake haɗa shi👇

 Ana so ka samo ko ka nemo ganyen Runhu wanda ya zuba a qasa da kansa, ma'ana ba wanda aka tsinko ba ko wanda aka hau kan bishiya aka ebo, a'a, wanda ake so shine wanda ya faɗo qasa da kansa, misali idan ka je gindin bishiyar zaka ga wasu ganyayyakin bishiyar sun faɗo qasa da kansu, su ake so, in ka samo su sai ka nemo ganyen daddoya da garin qaiqayi koma kan masheqiya, in an nemo waɗannan ganyayyakin dukkanin su sai a haɗa su a daka su a dinga yin hayaqi da haɗin, safe da yamma har zuwa lokacin da zai qare, shikenan, to wlh koda haɗi da turen aljani ko rauhani ko baqin jinnu aka yi maka zai lalace da yardar Ubangiji Allah, ni duk sirrukan da nake baku mafi yawancin su na Alqur'ani da sunnah ne da ganyen itatuwa da abubuwanda basu saɓawa Allah da manzon Allah ba ne, ayyuka ne masu kyau nake tura muku wallahi, ku dinga yin qoqari kuna yi idan dai har kuna fama da matsalarda kuka ga maganin ta.

Allah ya taimakemu ya rabamu da sihiri da jifa da hauka da wahala da tashin hankali da takaici da baqin ciki da talauci da yunwa da mummunar qaddara, ya Allah ka ɗaga musulunci da musulmai ka qasqantar da kafurci da kafirai, Allah ka taimake mu a rayuwar duniya da lahira ka zama jagoran mu, Allah ka jiqan iyayen mu ka haɗamu da su a aljanna 

Sannan kuma ina barar addu'o'inku duk wanda yaga wannan posting ɗin nawa a taya mu addu'a Qulhuwallahu qafa 10 Salatin Annabi qafa 10 hadiyya ga mahaifin mu da Allah ya yimasa rasuwa yau kwana 8, Allah ya gafarta masa da dukkanin musulmai.

Bayan haka waɗanda suke so a yi musu wannan aikin a haɗa musu haɗaɗɗen ganyan magarya da kainuwa dashen Allah, kokuma suke buqatar wani aiki da ya shafi matsalolin rayuwa na yau da kullum, ko matsalar soyayya ko aure ko matsalar kasuwanci ko matsalar sihiri ko matsalar abokanan tarayya ya tuntuɓe mu a wannan numbobin namu👇

08136560680 Call and WhatsApp

09020132884

Alhamdulilllah rabbil ãlamin

Follow us @shehudiezer (Facebook, Twitter, Instagram, TikTok, Snapchat)

Updated 14-06-2023
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url