Maganin Fitsarin Kwance Mujarrabun
MAGANIN FITSARIN KWANCE
Assalamu alaikum wa rahmatullah ta'ala wabarakatuh jama'a al'ummar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasallam, tsira da amincin Allah su cigaba da tabbata a gareshi har abada, Allah ka barmu da soyayyar Annabi kayi mana muwafaqa, kabamu komai mai amfani a garemu domin albarkacin Annabi.
Da sunan Allah mai rahama mai jin qai, yau dai ba tare da ɓata lokaci ba yau zan bayar da sirrin FITSARIN KWANCE ne, ko babba ko yaro ko mace ko namiji ko mai aure ko gwauro ko tsoho ko tsohuwa mai fitsarin kwance, Allah yana jarabtar wasu ɗaiɗaiku daga cikin mutane da fitsarin kwance koda kuwa a ce sun girma ko sun yi aure ko sun hayayyafa, jarrabawa ce daga Allah, wanda kuwa hakan ba qaramar matsala bace ga ɗan Adam, to cikin ikon Allah yau zan baku maganin Fitsarin kwance guda ɗaya zuwa biyu, kamar yanda Allah ya tabbatar cewa bai saukar da kowace cuta ba sai da ya fara saukar da maganin ta, to saboda haka in dai aka yi wannan aikin alfarmar Annabi da Alqur'ani za'a dace, kuma za'a samu cikakkiyar waraka mai dorewa, ga aikin na farko:
Da farko ana rubuta Ayatul Kursiyyu Qafa tara (9), amma ana yin rubutun ne wake wake, ma'ana qafa 3 da wasali za'a rubuta, qafa 3 ba wasali, qafa 3 ba wasali kuma babu ɗigo akan haruffan, a haka za'a rubuta ayatul kursiyyu ɗin, kunga kenan za'a rubuta Ayatul kursiyyu normal mai wasali qafa uku, Ayatul kursiyyu marar wasali qafa uku, Ayatul kursiyyu marar wasa marar ƴaƴa qafa uku, kunga jimilla zai bada qafa tara (9) kenan, idan aka rubuta sai a wanke rubutun, a samu Qasar Gidan Chinnaka/Kyashi a zuba a cikin rubutun a baiwa mai fitsarin kwancen ya dinga sha, ita kuma qasar da ta kwanta a cikin kofin sai a ebeta a dinga shafawa a marar mai fitsarin kwancen, kokuma a dinga bashi ya shafa da kansa in babba ne, Insha Allah a dinga yi masa haka akai akai baza'a ja dogon lokaci ba zai daina Insha Allahu ta'ala.
KOKUMA GA WANI MAGANIN FITSARIN KWANCE SADEEDAN DA YARDAR ALLAH
Idan an yi wancan shi kadai ma ya isa za'a samu waraka da yardar Allah, dukkanin su ayyuka ne masu qarfi, kuma ayyuka ne waɗanda basuda wata wahala, a cikin gidan ka ko gidan ki ma zaki iya yi, amma duk da haka ga wani zan qara muku, wanda Allah ya jarrabe shi da wannan matsalar ta fitsarin kwance yaro ko babba namiji ko macce mai aure ko marar aure to ga abinda za'a yi domin warkewa daga matsalar👇
Ana so a nemo ko a siyo fatar RAGON RUWA wata halitta ce wacce ana iya samun ta a wurin ƴan ganye da itatuwa masu siyar da magungunan gargajiya, idan aka basu Naira ɗari biyu (200) za su ebar maka fatar zasu baka, idan ka samu fatar sai ka zo gida da ita, yanda ake amfani da ita shine za'a samu RUWAN QAMZO idan nace ruwan Qamzo ina nufin ruwan da ake zubawa a tukunya idan aka kwashe tuwo daga cikin tukunyar, to wannan qamzon sai a zuba masa ruwa a tukunyar sai a ɗauko wannan ƴar fatar da aka siyo ta ragon ruwa sai a sakata a cikin ruwan qamzon amma a saka ruwan dai dai yanda mai fama da matsalar ko wanda yake fitsarin kwancen yaron ko yaran za su iya shanyewa, to idan fatar takai kamar awa ɗaya da rabi ko awa biyu a cikin ruwan Qamzon sai a cire ta daga cikin ruwan a ajiye ta sai a karanta “Bismillahirrahmanirraheem” qafa goma sha takwas (18) a cikin ruwan za'a tofa.
Idan lokacin kwanciyar yaron yayi kokuma lokacin kwanciyar mai fama da matsalar fitsarin kwancen ya yi sai adibi ruwan qanzonnan a bashi ya sha kokuma idan shi ya haɗa maganin da kansa in ya zo kwanciya sai ya sha, idan kuma yara ne su sha koda kuwa sun kai su goma (10) ne, kowa a cikin su a bashi cikon ludayin miya ɗaya (1) yasha, gobe ma a sake saka fatar a ruwan qamzon a basu su sha tsawon, jibi ma a qara saka fatar a cikin ruwan qamzo a basu su sha kwana uku kenan ake yin aikin, to Insha Allahu za'a rabu da wannan lalurar koda kuwa ta jinnu ce ko ta zama chronic za'a samu sauqi za'a daina wannan fitsarin da yardar Allah
A taimaka ayi sharing dan amfanin Al'ummar Annabi, a tura wa ƴan uwa da yayu da qannen mu maza da mata da qannen mu mata waɗanda suka yi aure domin su yiwa ƴaƴan su saboda gujewa yawan yin fitsarin kwance kokuma gujewa sabo da fitsarin kwance
Allah ya bamu sa'a ya sa mu dace duniya da lahira amin
Sannan kuma ina barar addu'o'inku duk wanda yaga wannan posting ɗin nawa a tayamu addu'a Qulhuwallahu qafa 10 Salatin Annabi qafa 10 hadiyya ga mahaifinmu da Allah yayimasa rasuwa yau kwana 8, Allah ya gafarta masa da dukkanin musulmai.
Domin neman qarin bayani game da wannan sirrin kokuma sauran sirruka wanda muka yi posting kokuma wanda yake so ayi masa wani aiki na mallaka ko karya sihiri ko matsalar miji ko iskokai ko neman mulki ko wanda yake son aure ko wacce take son aure budurwa ko bazawara, ko masu son ɗaukaka ko farin jini ko wanda yake da wata matsala ko damuwa namiji ko mace su tuntuɓe mu a wannan numbobin 👇
08136560680 (Call and WhatsApp)
09020132884
Follow us @shehudiezer on (Facebook, Twitter, Instagram, TikTok, Snapchat, etc.)
Alhamdulillah
Updated on 13-06-23