Maganin Ciwon Ciki Da Tsamukar Ciki

MAGANIN CIWON CIKI DA TSAMUKA DA AZABAR MURƊAWAR CIKI



Assalamu alaikum warahmatullah ta'alaa wabarakaatuhu jama'a alhullahi masoya sayyidil mursalina Sallallahu alaihi Wa sallama, Allah ya barmu tare da manzon Allah, Allah ya jiqan iyayen mu ya sa alkhairi a rayuwar mu, Allah ya taimakemu da taimakon sa ya bamu lafiya da zaman lafiya a qasar mu Nigeria da ma sauran qasashe da garuruwan musulmai baki ɗaya.

Wannan shekara ta 2023 ta kasance shekara da bazan yi qasa a guiwa ba wurin taimakawa mabiya wannan shafin nawa mai albarka, Insha Allahu sai na cika fuskokin ku da farin ciki da annashuwa, ku kasance tare da ni shehu diezer, sannan kuma waɗanda suke so ayi posting ɗin wani sirri ko wani magani wanda basu gan shi a cikin wannan page din nawa ba zasu iya yin comment a qasa, nikuma Insha Allahu zan shirya wannan posting game da wannan matsalar in ɗora a wannan shafin mai albarka.
Ba tare da ɓata lokaci ba yau nazo muku da magani ne naciwon ciki da azabar ciki da wahalarwa mai tsanani game da murɗawar ciki, duk wanda ciwon ciki ya kama shi sai ya samu ruwa a cikin kofi, kokuma a samu ruwa cikin kofi a tofamusu suratul Kafirun “Qulyã ayyuhal kafirun” har zuwa qarshe qafa 7 sai a baiwa mai fama da ciwon cikin ruwan yasha, Insha Allahu ciwon cikinnan zai dauke nan take bada jimawa ba, zai fara zufa da gumi Insha Allah zai samu lafiya

Kokuma a rubuta “FA ASÃBAHÃ I'ISÃRAN FEEHI NARUN FAHTARAQAT” qafa arba'in da ɗaya (41) a wanke a samu sassaken bishiyar TSAMIYA a daka shi sosai har sai ya zama gari, in ya zama gari sai a saka a cikim ruwan rubutunnan asha, in Allah ya yarda daga ranar kã daina ciwon ciki Insha Allahu.

GA WANI MAGANIN CIWON CIKI MUJARRABUN 👇

Mafi yawancin mutane suna fama da yawan ciwon ciki babu gaira babu dalili, mutum ya rasa yadda ma zai yi idan cikin sa yana ciwo , ya rasa inda zai sa kansa, gaa yadda zaku yi Insha Allah, dukkanin sirrukan guda uku da na bayar duk babu wanda baya maganin ciwon ciki kowane iri ne a cikin su.

Da farko zaka samu ruwa mai kyau mai tsafta a cikin kofi ka karanta Fatiha qafa bakwai (7) ka tofa a cikin ruwan kasha ko abawa wanda cikin nasa yake ciwo ya sha, Insha Allahu zai samu waraka nan da nan da yardar Ubangiji

Kokuma idan mutum cikin sa yana yi masa ciwo ya samu ko a samu ruwan zafi a sa zuma a cikin ruwan zafin sai a karanta Fatiha qafa bakwai 7 a cikin ruwan zafin mai zumar, in an gama tofawa sai a sha ko a bawa wanda cikin nasa yake ciwon yasha gabaɗaya Insha Allah cikin gaggawa zai samu waraka da yardar Ubangiji Allah

 Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya amin summa amin, Allah ya bamu ili mai amfani na taimakon al'umma, Allag ya bamu abunda zamu dogara da kanmu, Allah ya sa mu cika da imani, Allah ya bamu haquri da juriya da jajircewa akan gaskiya alfarmar Annabi da Alqur'ani, Allah ya rabamu da talauci yayi mana silar arziqi dan hasken Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama.

Muna yiwa jama'a ko wane irin aiki su bayar da abun sadaka, in dai na magunguna da asirai ne, da aikin addu'o'i da shawarwari, duk wanda yake da wata kalar buqata game da matsalar aure ko soyayya ko firaqu ko kasuwancin sa ko takararda yake yi a garinsu ko a qasar su ko ƴan siyasa ko dafa'i ko jalabi ko istihara ko Ramli da binciken rayuwa da binciken lamarin aure da gane yanda aure zai kasance duk ina yi cikin iko da iyawar Allah, idan ka gayamun sunanka da na mahaifiyarka to ba tare da na sanka ba ba tare da ka yimun bayani ba ba tare da wani ɓata lokaci ba zan gaya maka halayen ka majority ɗinsu da kamannin ka da komai naka abubuwanda kake so da abubuwan da baka so, da dabi'uka da matsalolinka duka.
Sannan kuma bugu da qari akwai waɗansu magunguna kala daban daban masu inganci a cikin wannan shafin nawa idan kunje chan qasa kokuma kun koma chan sama zaku gansu bila adadin, kuma wanda yake so ya cigaba da amfanuwa da sirrukan mu to zai iya saving din bookmark na website ɗin namu a browser da yake amfani da ita, duk lokacinda yake so yazo ya ɗauki wani sirri sai yaje ya duba bookmark ya shigo domin duba new update a page din
Domin neman qarin bayani kokuma masu so a yi musu aikin to sai su tuntube ni akan numbobina na kira kokuma akan WhatsApp a wadannan numbobin nawa👇
08136560680
09020132884

Duk Wanda yake da tambaya sai yayi comment a qasa da tambayar tasa kokuma ya kirani a waya 08136560680, ko 09020132884, Allah ya sa mu dace duniya da lahira ameen.



Follow me on Facebook: www.facebook.com/shehudieza
Instagram @ www.instagram.com/shehudiezer
Twitter www.twitter.com/shehudiezer
Tiktok www.tiktok.com/shehudiezer
YouTube: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819 
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url