Maganin Iska Da Aljanu Da Almatsutsai

MAGANIN ISKA DA ALJANU


Assalamu alaikum warahmatullah ta'ala wabarakaatuh jama'a al'ummar musulmi, barka da wannan lokaci, Allah ya sada mu da alkhairai da abubuwan farin ciki da suke cikin wannan rayuwar ya kuma tsaremu daga sharrukan da suke cikinta.

Yau na zo muku da maganin ISKA ko ALJANI guarantee, wanda/ wadda iska ya dameta namiji ko mace, babba ko yaro, tsoho ko tsohuwa, budurwa ko saurayi, sai a jarraba wannan babban aikin Insha Allahu za'a rabu da matsalar Iska har abada, a nustu sosai a karanta, aikin yana da wahala kaɗan, yana da sarqaqiya, abunda duk ba'a ganeba a kirani a waya 08136560680, ko ayi comment.

Da farko ana so a samo kããshin mahauta, idan mutum yaje kasuwa yaje mahauta zaiga inda ake tara kããshin tumbin dabbobi, inda ake zubar da kaashin tumbin dabbobinda ake yankawa, to sai a ebo wannan kaashin, sannan kuma a samu tsakin miyar kuka, tsakin miyar kuka ana samun shi ne idan mata sun tankaɗe miyar kuka suna barin tsakin miyar da suka tankaɗe, to wannan tsakin da ake tarawa in an gama tankaɗe miyar shi ake so, idan kuma baka samu tsakin kukar ba zaka/ zaki iya zuwa kasuwa kisiyo kuka wadda ba'a daka ba sai kazo/ kizo gida ki dakata ki tankaɗe sai ki cire tsakin kiyi amfani da shi, bayan an samu tsakin sai a haɗa shi da wannan kããshin da aka ebo a mahauta, bayan an haɗashi da kashin mahautar sai a nemo qaiqayin gero , za'a iya zuwa inda ake yin sussukar gero, a chan ake samun qaiqayin geron, a ebo wannan qaiqayin da ake tarawa bayan an sheqe gero, in an ebo shi sai azo a haɗa shi da wannan Kããshin mahautar da Tsäkin miyar kuka da aka samo, a haɗa su wuri ɗaya, ma'ana a haɗa Kããshin mahauta da Tsakin kuka da qaiqayin gero wuri daya, bayan an haɗasu sai a daka su su daku, sai a samu Jan Miski a haɗa a chakuɗa shi dasu duka, sai ayi wanka a dinga hayaqi da shi, ga hoton jan miskin nan a qasa zan nuna muku saboda idan kun je siyowa ba sai kun sha wahala sosai ba👇


             Wannan👆 shine Jan Miski


Duk wanda iska ya dame shi ko wadda iska ya dame ta to a haɗa mata wannan aikin a sakata taje tayi wanka sai azo a yimata hayaqinnan, koda kuwa tana ihu ne tana faɗa tana buge buge to a sakata dole sai ta dinga yin hayaqin, koda ace sai an rirriqe ta ne arirriqe ta a dinga yi mata hayaqin ta qarfi da yaji, to in ana yin haka Insha Allahu ta'ala zata rabu da wannan matsalar cikin gaggawa, Aljanu da kansu firgita suke yi da shiga mugun bala'i idan suka ji wannan haɗin, wannan haɗin azaba ne ga Aljanu, Insha Allah zata samu sauqi iskan zai bar jikin ta har abada alfarmar Annabi Sallallahu alaihi Wa sallama.
Allah yabada sa'a.
Waɗanda suke so a haɗa musu wannan aikin su kirani a waya 08136560680 kokuma 09020132884 kokuma suyimun magana a WhatsApp da numbar 08136560680, Insha Allah za su biyan buqata, zamu haɗa musu zamu aika musu shi har inda suke, in kuma mutum zai iya hadawa da kansa alhamdulilllah, in ma wani aiki mutum yake so a yimasa to ya yimun magana a numbata ya kirani Insha Allah za'a yi masa.
Ga wani maganin Aljanun:

Wannan maganin mujarabun ne Insha Allahu, yana maganin jinnu ko wanne kalar jinnu ne ko wane kalar iskokai ne koda kuwa sun shekara ashirin a jikin mutum wannan sirrin yana yin maganin su cikin sauqi da yardar Arraheemu

Wannan maganin ba maganin Jinnu kawai yake yi ba, yana yin maganin:

* MAGANIN FARFADIYA 
* MAGANIN NAMIJIN DARE
* MAGANIN ISKA MAI SAKA MUTUM SURUTAI 
* MAGANIN DUK WATA MATSALA TA ISKA 

To da farko dai za ka samu waɗannan abubuwan da zan ambato kamar haka:

Ana samun mataccen jemage guda ɗaya, ana samun yayin gidan tururuwa babba, yayin gidan tururuwar babban gidan tururuwa ake so, sannan kuma ana samun busashiyar jaɓa guda daya, sai kuma a samu jan kajiji, sai kuma a samu
BAQIN KAJIJI Sai kuma a samu Qashin angulu, sannan kuma ana samun HALTITI NA QWAYA guda bakwai za'a samu, sai a qarshe ana samun DADDAWA wadda aka mulmulata tayi circle tayi zagaye, banda wacce tayi fãɗi, sai a haɗa su dukkanin su ka haɗa su ka daka su dakan hayaqi sama sama za'a daka su, sai ka samu turaren NURUL JINNI ka saka shi a cikin wannan haɗin da ka daddaka, idan ka gama aikin ka gama haɗa su sai ka samu sabuwar kwarya kokuma SABON qoqo ka saka shi wannan haɗin a cikin sa, kada ka kuskura ka bar maganin a cikin leda kokuma a cikin kwano ko roba ko kwali ko takarda, hakan zai iya lalata shi ko ya ɓata shi, a kula sosai.
To bayan an yi haka dan Allah duk wanda ko wadda take da ɗaya daga cikin waɗannan matsalolin na iska ko farfaɗiya ko namijin dare ya dinga yin hayaqi kokuma a dinga yi mata hayaqi da shi kullum sau biyu a rana wallahi ko mutum yana fita waje da gudu ana bin sa ana kamo shi ana dawo da shi gida to da yardar Allah zai samu lafiya wannan sirrin mujarabun ne kuma yawancin waɗannan abubuwan da na ambata duk ana siyar da su wajan masu magunguna da itatuwa, Allah ya taimakemu yasa mu dace summa amin.

Muna qara sanar da ku cewa muna yin ko wane irin aiki ne in dai bai saɓawa shari'a ba, kar wannan damar ta wuce ku, in dai aiki ne na magunguna da asraru da addu'o'i da shawarwari ne to muna yin su duka, duk wanda yake da buqata game da matsalar aure ko soyayya ko budurwar sa ko matar sa ko firaqu ko kasuwancin sa ko takara ko dafa'i ko jalabi ko istihara ko Ramli da binciken rayuwa da binciken aure da gane yanda aure zai kasance duk muna yi cikin iyawar Allah da sahalewar sa, 

Domin neman qarin bayani kokuma waɗanda sukeso inyimusu wannan aikin ko muhaɗamusu wannan maganin ko muyimusu wani aiki nawata damuwarsu sai su tuntuɓeni kokuma a yi comment ko a kirani a waya 08136560680, 09020132884 (Call and WhatsApp)

 Ga link na WhatsApp group dinmu:
YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawaAlhamdulillah
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url