Maganin Sanyi

 MAGANIN SANYI NA MARA KO SANYIN GABA

Assalamu alaikum jama'a mabiya shafina na shehudiezer ina gaisheku ina yimuku fatan alkhairi duniya da lahira Allah yasa mudace yasa mukasance tare da Annabi Muhammadu Rasulillahi Amin.

 Yau dai wannan maganin sanyi ne na kawomuku, maganin sanyi na mara da sanyi wanda yake hana dadewa ana yin jima'i, wannan sirri ko sirruka da zan bayar Insha Allahu maganin dadewa ana jima'i ne kuma maganin qarfin maza ne, domin idan ka samu lafiya ingantacciya to kasamu qarfi ba shakka.

Ba tareda ɓata lokaci ba za'a je kasuwa inda ake siyarda kayan miya da kayan lambu a siyo CITTAR CURRY ɗanya akeso ba busassa ko niqaqqa ba, ƴar madaidaiciya ba mai yawa ba, cittar kori itace wacce ake kira da Turmeric da turanci, ga hotonta zansaka a qada👇

Idan an samo wannan cittar kori ɗin sai a samo ɗanyar citta itama ɗanta akeso ƴar madaidaiciya ba mai yawa sosai ba, itama ga hotonta 👇


Bayan an samosu duka su biyu sai a siyo Tafarnuwa da Kanumfari suma kamar na ɗari ɗari, in an siyo duka sai adawo gida asamu turmi awanke cittar kori ɗinnan da ɗanyar citta da tafarnuwar asanyasu a turmin kokuma a naɗesu a buhu mai kyau aɗan daddakasu samasama su ɗan daku, bayan sun daku sai a zubasu acikin tukunya azuba ruwa kamar rabin bokiti sai asaka kanumfarinnan adora akan wuta abarshi yadahu yadahu sosai sosai, bayan ya dahu sai a tace ruwan maganin adinga sha qaramin kofi safe da yamma har yaqare, kafin yaqare za'a rabu da wannan ciwon sanyin da yardar Allah

Idan kuma misali namiji ne mai aure zaiyi aikin maganin yanaso maganin yayi qarfi sosai yazama maganin karfin maza yaqaramasa lafiya da kuzari to sai yahaɗa da namijin goro guda 3 ko 2 ya daddaka yadafa taredashi sai ya tace yadinga sha, wallahi matarka ta shiga uku domin sai tasha azaba saboda qarfi da jimawa, Wannan maganin dadewa ana jima'i ne, kuma maganin sanyi kowane iri ne sahihi ingantacce.

Domin neman qarin bayani kokuma masu tambaya sai su kirani a waya ko suyimun magana a WhatsApp 08136560680 kokuma 09020132884

Kuyi haquri nayi alkawarin zan kawo maku yadda ake yin Istihara ta asali ba jabu ba, amma kuma har yanzu ban kawo ba, hakan yaci tura, ansamu matsala ne ban gama haɗa bayanan istiharar ba shi yasa banyi posting ba, dan Allah ina neman afuwa akan hakan.

Sannan kuma bugu da qaari akwai waɗansu magunguna kala-kala acikin wannan shafin nawa idan kunyi aqasa kokuma kunyi sama zaku kallesu, kuma kuyi saving din bookmark na page ɗin nawa a browser dinka domin duba new update a page din

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url