Sirrin Karya Sihiri Na Maza Da Mata Mujarrabun (II)

SIRRIN KARYA SIHIRI NA MAZA DA MATA MUJARRABUN (II)


Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu, jama'a ƴan uwana maza da mata al'umma masoya manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama, da fatan kuna cikin qoshin lafiya da amincin Allah da yardarsa ,Allah yasa haka ameen ameen.

Kamar kullum dai muna jan hankalinku ayyukanda muke baku kudinga turawa ƴan uwanku domin su amfana, ku dinga sharing ku dinga jarabawa, kar kace aikin yayi wahala ba zaka iya ba, ka daure ka gwada, wataqil nan ne warakarka take wataqil qin yin aikin da kayi shine babban kuskurenda zaka yi a duniyarka ta asraru da magunguna.

Bayan haka yau dai sirrinda na kawomuku wani gagarumin sirri ne wanda ya samo asali daga wurin manya manyan malamanmu da iyayenmu, irin waɗannan sirrukan wallahi ko a littafi ba zaka samesuba, kuma babu wanda zai gaya maka sai wanda ba yada qeta kuma bayada rowa, kuma saboda yanayin da nake gani kwanakinnan Mazambata sunyi yawa acikin harkar addu'oi da taimakawa al'umma a internet, mutane suna cuta tareda danne haqqin jama'a da yaudararsu, akula da ƴan Damfara sosai masu satar posting da masu cewa zasu yimaka aiki kuma suqi yi, saboda haka shiyasa nace bari in qara kawo muku tawa gudummawar domin al'ummarmu a yanzu babu abunda yafi zama matsala a garemu kuma ya zama ruwan dare kamar SIHIRI da MAKARU da JIFA da TSIBBU da KAMBUN BAKA, to Insha Allah duk wanda zai iya yin wannan wuridin zai dace alfarmar manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, wannan sirrin shigen irin sirrinda na baku ne na Ya qahharu na allon qarfe, shima wannan aiki ne wanda ake yinsa da allon qarfe komai nasa kusan ɗaya yake da wancan aikin, banbancinsu bashida yawa sosai.

To dafarko dai za'a samu Allon Qarfe a wankeshi sai a rubuta wannan ayar👇 

“MÃÃ JI'TUM BIHIS SIHR, INNAL LAHA SAYUBƊILUH, INNAL LAHA LA YUSLIHU AMALAL MUFSIDEEN” Qafa ɗaya (“1”) da tawada za'a yi rubutun, amma za'a qarawa dukanin Mimun mimun na cikin wannan ayar girma, ta yanda za'a iya rubuta sunan wanda akeso a karyawa sihirin a ciki kamar yadda zaku gami a qasa misalin wannan hoton naqasa👇


Bayan anyi rubutun a jikin Allon Qarfen sai a samu wutar garwashi kokuma wutar mangal ko makubur, kokuma murhu mai garwashi sosai tayanda za'a iya daura allon akan garwashi yasha zafi sosai.


In aka samu wutar sai ayi arwala, a samu abokanai waɗanda zasu kama maka wurin yin wannan wuridin a gaban wutar inda kaɗora allon qarfen, it's recommended a tayaka domin wuridin yanada yawa gaskiya, amma in mutum yaga zai iya yi shi kaɗai har ya gama wannan adadin ma abun yaa wadatar alhamdulillahi, anfi son haka, bayan anyi arwala sai a shimfiɗa abun zaunawa mai tsarki ko tabarma kokuma sallaya ko buzu, ko wani abun yin sallah mai tsarki, sai a ɗora Allon Qarfen akan garwashin sai ayi Bismillah da Fatiha da Ayatul kursiyyu sai kuma ayi Istigfari qafa ɗari {100}, Salatin Annabi qafa {100}, La ilaha illallah qafa ɗari {100}, bayan an gama istigfarim da Salatin da hailala sai a fara wuridin wannan ayar rubutun da aka rubuta ajikin allon qarfen,gatanan darubutun Hausa nayita amma da larabci za'a rubuta ajikin allon qarfen👉 “MÃ JI'TUM BIHISSIHR, INNALLAHA SAYUBƊILUH, INNALLAHA LA YUSLIHU AMALAL MUFSIDEEN” za'a yi wuridin wannan ayar Qafa 12,000 dubu goma sha biyu ana yi ana maimaitawa har a gama allon yana kan wuta yana shan zafi sosai, in an gama wuridin gaba ɗaya sai ayi addu'a akan buqatarda ake nema sai a sauke allon a barshi a gefe kawai.

Wallahi tallahi wannan sirrin mujarrabine mun gwadashi munci moriyarsa sosai wallahi, maza da mata da tsofaffi da yara da manya da kowa zai iya amfani dashi, kokuma za'a iya yimasa kuma zaimasa amfani, Dafa'i ne na kaariyar jiki daga sihiri wallahi, Allah yataimaka, na badashi kyauta domin Allah, domin Manzon Allah (SAW), kowa yayi kuma yayiwa yan uwansa domin yanzu duniya ta lalace maqiya sun rinjayemu, duk wanda yayi amfani da wannan sirrin tabbas zai ci amfaninsa kuma zai ga biyan buqata alfarmar manzon Allah, kuma dan Allah ayimun Addu'a inkasanu biyan buqata, abubuwanda suke damuna Allah ya yayemun ya kawomun mafita, Allah ya kawomana mafita yabamu aikin yi ya tsaremu da tsarewarsa ya kiyayemu ya yimana gafara bakiɗaya don darajar Annabi SAW.

Waɗanda kuma suke da wata matsala ta neman aure kokuma neman soyayyar wanda suke so kokuma wata damuwa kokuma suke so ayi musu wannan aiki kuma muna yiwa mutane sai su biya abun sadaqa saboda yanayinda muke ciki, ba kowa ne zai iya tsayawa yayi ba, to sai ya bayarda abun sadaqa ayi masa ba cuta ba cutarwa zamu taimaka mu tsaya mu yiwa mutum domin Allah tsakani da Allah domin rage wahalar a gareshi, domin ba kowa yakeda lokacinda zai tsaya yayiba sai A kirani a numbata 08136560680 (WhatsApp) 09020132884 (Call), INKUMA NUMBAR TAWA AKA KIRA AKAJI A KASHE TAKE KOKUMA BATA SHIGA SAI A TURAMUN SAQO (TEXT) KOKUMA A TUNTUƁENI TA WHATSAPP DA NUMBAR ZA'A SAMENI INSHA ALLAHU, DOMIN TABBAS INA TAFIYA LOCAL GOVERNMENT ƊINMU HUTUNE YAKE KAINI CHAN A LOKACIN SALLAH KOKUMA KOKUMA WASU PUBLIC HOLIDAYS, in kuma mutum zai iya yi alhamdulillahi komai yazo cikin sauqi gashinan sirri guarantee naa bayar don Annabi SAW, muna sadaukarda lokacinmu da ayyukanmu da datarmu da hannuwanmi da idanuwanmu muna yin posting domin ku amfana, Allah yasa musamu ladar taimako ya sakamana da alkhairi, kudinga sakamu a addu'a.

Domin neman qarin bayani kokuma masu neman muyi musu wannan aikin na karya sihiri ko mallaka ko wacce takeson yin aure ko maganar kasuwanci, sai su tuntubeni akan numbers ɗina kokuma akan WhatsApp a wadannan numbobin nawa na qasa👇

08136560680

09020132884

Duk Wanda yake da tambaya sai yayi comment aqasa da tambayarsa, Allah ya sa mu dace duniya da lahira amin.

Ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn

Follow me on Facebook: https://www.facebook.com/shehudiezer1

E-mail: alameengobeer1@gmail.com

Instagram: https://www.instagram.com/shehudiezer

Twitter: https://www.twitter.com/shehudiezer

Tiktok: https://www.tiktok.com/shehudiezer/

Threads: https://www.threads.net/@shehudiezer

YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa


Alhamdulillah

Next Post Previous Post
1 Comments
  • Unknown
    Unknown October 28, 2021 at 3:07 AM

    Muna Godiya Allah Yasaka Da Alheri

Add Comment
comment url