Wuridin Yasin Mai Qaharu (Tilastawa)

WURIDIN YASIN MAI QAHARU (Tilastawa) Assalamu alaikum warahmatullah ta'ala wa barakatuh jama'a barkan ku da wannan lokaci da fatan kuna lafiya, Allah Ubangiji yasa haka amin amin, Allah ya qaro mana lafiya da nisan kwana da albarka alfarmar annabi SAW yau ma dai na zo muku da babban sirri na Yasin mai qaharu domin tilastawa kokuma rinjaye da tirsasa wank mutum yayi wani abu wanda ake so, kokuma ya bayarda goyon bayan wani abu wanda ake so kokuma ya amince da wata buqata da ake so
Bayan haka yau nazomuku da wannan sirri babba domin biyan buqatarku batareda shan wahala ha da yardar Allah,wannan sirrine yna YASIN MAI QAHARU (tilastawa),

To dai ita YASIN MAI QAHARU addu'a ce ko ince wuridi ce wacce ake yinta idan ana neman rinjaye akan wani ko wata l, ana yinta ne in ana neman galaba ko nasara akan wani ko wata, game da karɓar kuɗi ko karɓar bashi ko tilastawa mutum yayi maka wani abu wanda kake so, haka zalika ana yinta domin neman aure ko neman mulki ko neman wani matsayi ta hanyar wani, ko rinjayen shari'a agurin Alqali kokuma duk wani abu da kake neman rinjaye a kansa, amma a ji tsoron Allah, kar ayi domin damfarar wani ko cutar wani ko karɓar abun wani da niyyar ba za'a biyashi ba a qi bashi, hakan ya saɓawa musulunci kuma hakan cin amana ne da cin zalin, kuma Allah ya hana, Manzon Allah SAW ya hana cin haqqin wani ya hana zamba cikin aminci ya hana cin duniyar wani.

To shi dai wamnan aikin ana yin wuridin ne qarfe ɗaya na dare, ana fara wuridin ne da abubuwa kamar haka;

Istigfari qafa ɗari (100)

Salatin Annabi qafa ɗari (100)

La ilaha illallah qafa ɗari (100)

Bayan an gama Istigfarin da Salatin Annabi da La ilaha illallahu sai a karanta Tahiya qafa bakwai (7), wannan itace tahiya zan rubuta muku ita da hausa👇

“Attahiyãtu lillahi, azzãkiyãtu lillahi, aɗɗayyabãtus salawãtu lillahi, Assalamu alaika ayyuhan nabiyyu, warahmatullahi ta'ala wa barakãtuhu, assalamu alaina, wa alã ibadullahis Salihina, Ash-hadu an la ilaha illallahu wah dahu lã sharika lahu, wa Ash-hadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu“ Qafa 7.

Bayan an gama waɗannan addu'o'in sai a fara wuridin na yasin Qafa goma sha ɗaya (11), amma kuma kowace aya in aka karantata sai ance “YÃ QAHHÃHU TAQAHHARTA BILQAHARI WALQAHARU QAHHIR QAHHARAKA YÃ QAHHÃRU” Qafa ɗaya (1) a bayan kowace aya, misali in nafara Bismillahir rahmanir raheem YASEEN YÃ QAHHÃHU TAQAHHARTA BILQAHARI WALQAHARU QAHHIR QAHHARAKA YÃ QAHHÃRU, WAL QUR'ANIL HAKEEM YÃ QAHHÃHU TAQAHHARTA BILQAHARI WALQAHARU QAHHIR QAHHARAKA YÃ QAHHÃRU, INNAKA LAMINAL MURSALEEN YÃ QAHHÃHU TAQAHHARTA BILQAHARI WALQAHARU QAHHIR QAHHARAKA YÃ QAHHÃRU, ALÃ SIRÃƊIN MUSTAQEEM YÃ QAHHÃHU TAQAHHARTA BILQAHARI WALQAHARU QAHHIR QAHHARAKA YÃ QAHHÃRU, a haka a haka za'a cigaba har a gama.

in an gama wuridin Yasin ɗin gabaɗaya ana yin sadaqa mai qarfi kokuma a yanka Zakara ko Kaza, rashin yin sadaqa naqasu ne acikin wannan aiki, ku tabbatar bayan kun yi wannan aikin kun yi sadaqa mai girma mai qarfi. 

Bayan anyi sadaka sai ajira kamar bayan kwana biyu ko kwana uku sai aje a samu wanda ake neman wani abu agurinsa, wanda akayi aikin akansa a tambayeshi ko ace yayi abunda aka qudurta Insha Allah zaiyi komai da yardar Allah.

Sannan kuma bayan haka masu buqatar a yimusu wannan aikin su bayar da abun sadaqa sai su tuntuɓeni akan wannan numbar 08136560680, in kun kira kunji wayar tawa a kashe sai ku tuntuɓeni da numbar a WhatsApp zaku sameni, kokuma a numbata ta Zain 09020132884, waɗanda kuma suke da wata buqata ta daban zasu iya kira suyi bayani Insha Allah zamu yi qoqarin maganin wannan matsalar alfarmar annabi SAW.

Allah yabada sa'a kuma Allah yabiya mana buqatunmu na alkhairi duniya da lahira

Allah yasa buqatocinmu na alkhairi duniya da lahira subiya,

Allah yaqaramana lafiya da zaman lafiya,Allah yayayemana masofa da bala'i amin.

Wanda yakeda tambaya ya tuntuɓeni

08136560680 (WhatsApp and Call 🤙)
09020132884

Bayan haka ina kira gareku mabiya shafin shehu diezer, wasu daga cikinku abunda suke yi bai kamata ba kwata kwata, zasu kira wayata domin suyi tambaya kokuma a yimusu wani aiki wai sai suyi mun flashin maimakon su saka kati sukira, wannan ai wulaqanci ne da rashin sanin muhimmancin abunda kake nema, ta yaya zaka yimun flashin inba wulaqanci ba, ka ari wayar wani wanda yakeda kati ka kira idan bakada kati amma ba wai kayimun flashin ba, a wasu lokutan ma idan naga flashin din ina yin qoqari wajen kiran numbarda ta yimun flashing ɗin, amma abun mamaki sai kaga na kira aqi yin magana kokuma aqi ɗauka kokuma a ɗauka ayita janka da surutu mara amfani, kokuma kakira a yita yimaka abunda zai ɓatamaka rai, wannan ai rashin mutunci ne ga ilimi wallahi, kuma duk wanda yayimun flashin bazan samu damar kiransa ba gaskiya, saboda muma abinci muke nema abunda zamu dogara da kanmu muke nema a kowanne lokaci, masu yin haka dan Allah su kiyaye, bana jin daɗin haka kokaɗan wallahi.

Dan Allah a kiyaye

Bayan haka ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
Tiktok: 
YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa


shehudiezer ✍️
Next Post Previous Post
3 Comments
 • mtahir clothig
  mtahir clothig January 19, 2022 at 6:39 AM

  allah kabiyaka

 • Shehudiezer
  Shehudiezer July 1, 2022 at 8:36 AM

  Ameen

 • Anonymous
  Anonymous November 2, 2022 at 3:15 PM

  Allah yasaka da alkhairi

Add Comment
comment url