Maganin Farinjini Da Samun Shahara Acikin Al'umma

SIRRI / MAGANIN FARIN JINI DA SAMUN SHUHURA ACIKIN MUTANE DA AL'UMMA

Assalamu alaikum warahmatullah ta'ala wabarakaatuh, ƴan uwa mata da maza barkan ku da wannan lokaci dafatan kuna cikin qoshin lafiya, aminci da biyan buqata, ina yi muku fatan alkhairi a duniya da lahira, ina yi muku addu'a Allah ya biyawa kowa buqatun sa na alkhairi, Allah yasa mu gama lafiya, Allah yamagance mana matsalolinmu ameen ameen.

Ina samari masu neman farin jini amma abu ya gagara, ina ƴan mata masu neman farin jini amma abu yaci tura, ina zawarawa masu neman farin jini domin samun mazajen aure amma sun gagara samu, ina ƴan kasuwa masu neman farin jini domin kasuwancin su yayi farin jini a sanadiyyar su amma sun rasa yanda zasu yi, ina Jarumai na film da na masana'antu da ƴan wasan kwaikwayo masu neman sanayya da farin jini, ina ƴan social media da activist da ƴan facebook da twitter da YouTube da sauran su masu neman farin jini masu so asan su a duniyar shafukan sada zumunta da sauransu, yau dai nazo ne domin ku, domin nazo ne in sakar muku wasu manyan sirruka na FARIN JINI Mujarrabai guda 2 wlh, mun gwada su mun ga amfanin su sosai a rayuwa

Wlh koda mutum maqiyin ka ne in dai kayi wannan sirrin to cikin ikon Allah da buwayarsa sai yaji yana qaunarka aran sa, kokuma sai yaga komai naka yana burgeshi, sai kuma yaji kana burgeshi, sirrukan farin jini yawa ne dasu waɗanda muka jarraba muka ga aikinsu, wallahi akwai wani abokina da har jimasa ciwo aka yi aka ce yana yiwa mata asiri, daga yaaje wani gari ziyara, sanadiyyar wani sirri na farin jini da yayi, amma wannan mai sauqin ne daga cikinsu wanda yakeda kaifi sosai.

Ga yanda ake yin aikin na farko👇Wannan hatimin na sama👆 ana rubuta shi qafa ɗaya (1) ranar Litinin (Monday), bayan an rubuta shi a ranar za'a yi wanka dashi a tsakanin sallar Magriba da Isha'i a wuri mai tsarki za'a yi wankan ba a banɗaki ba.

To in dai an yi wannan da yardar Allah a jira aga ikon Allah, zuwan jama'a, soyayyar maza da mata, in sana'a kake yi zaka ga jama'a suna son zuwa wurin sana'ar ka. 

Ga yanda ake yin aikin na biyu👇

A kula, dukkanin waɗannan ayyukan masu kyau ne mujarrabai ne, sannan kuma daban daban ne ba a tare suke ba, basuda wata alaqa, kowanne aiki a cikin waɗannan ayyuka guda biyu zaman kansa yake yi.

Ka tabbatar lokacinda zaka yi wannan aikin akwai hasken farin wada daren goma ko daren sha ɗaya ko daren sha biyu har zuwa daren 20 ga wata 

Da farko shidai wannam aikin na biyu na rubutu ne, rubutu ne wanda ake aiki dashi kuma ana samun nasara ba shakka, amma wannan sirrin na biyu yanada haɗari gaskiya, kuma yanada qarfi sosai fiye da tinani.

Ana so a samu zuma mai kyau mai inganci, wacce batada mix batada haɗi kokaɗan, bayan an samu zumar sai a samu wanda zai rubuta maka SURATUL YUSUF qafa bakwai (7) kokuma qafa goma sha ɗaya (11), amma na qafa sha ɗayan ya fi qarfi gaskiya, rubutu mai kyau ba rubutu na ganin dama ba, kar ka baiwa waɗanda za su yi maka rubutu mara kyau kokuma rubutu wanda ba cikakke ba, in zaka iya nutsuwa ka rubuta dakanka to alhamdulillah anfi son hakan, in kuma ba zaka iya ba sai ka bayar a rubuta maka amma ka tabbatar waɗanda ka baiwa zasu rubutamaka zasu yimaka mai kyau sosai, in aka yi ha'inci a rubutun ko son rai ko aka qi cika rubutun dai dai to ba lallai in anyi aikin yayi yanda ake so ba.

Bayan an rubuta maka SURATUL YUSUF ɗin qafa bakwai 7 kokuma qafa goma sha ɗaya sai ka zuba rubutun a cikin tasa ko kwano ko silver mai kyau mai tsafta sai a ɗora kwanon a saman rufin kwano ko rufin gida ko akan gini ko akan katanga kokuma duk inda rubutun zai samu isasshen hasken farin wata ya kwana yana haskashi har zuwa alfijir ko lokacin asuba, koda a tsakar gida ne in dai an tabbatar wurin yana da tsarki kuma babu wanda zai buge rubutun ko ya zubar ko ya taka, to za'a iya shanyawa a gurin, in so samu ne ana so ka samu glass fari wanda zai rufe kwanon amma ba zai hana hasken farin wata ya haska rubutun ba, ko farar ledar pure water babba, kokuma wani abu wanda ba zai hana hasken farin watan ya haska rubutun sosai ba, kokuma kawai a shanya rubutun a haka, ba wani matsala yin hakan, ana so yasha hasken farin wata har zuwa asuba, idan aka yi sallar asuba kafin rana ta fito sai ka ɗauko wannan ruwan rubutun da aka shanya da wannan zumar da ka nemo ko ka siyo sai kayi bismillah ka zuba zumar a cikin rubutun, asamo zumar sosai domin ana so rubutun yayi zaqi sosai, in an zuba zumar sai a motsa sosai, in an motsa sai a shanye rubutun amma a raga ɗan kaɗan wanda za'a shafawa jiki, a shafe jiki duka da sauran rubutun da aka rage.

Bayan an yi haka shikenan aikin ya kammala, a jira ijaba ta farinjini da soyayya da qauna daga mutane daban daban da jama'a daban daban, wallahi Allah wannan sirri ne mai qarfi sosai kuma sirri ne mai zaman kansa, in kayi wannan aiki kasha shi kanka zai iya yin ciwo kokuma maqogoronka yayi ciwo ko kayi zazzaɓi ko ciwon kai, alamomin nasara ne in kaga haka Insha Allah, qarshen bayanin kenan

Masu tambaya ko masu neman qarin bayani zasu iya yin tambayar su a comment kokuma su kirani a waya su tambayeni kokuma su yimun magana a WhatsApp

Sannan kuma mutane waɗanda sukeso muyimusu wani aiki na sirri kokuma wani aiki dabann zasu iya yimun magana a WhatsApp kokuma ku kiramu awannan numbonin namu 08136560680 ko 09020132884 kokuma su yimana magana ta WhatSApp 08136560680 Masu neman wasu sirruka na Shehudiezer zasu iya yin qasa zasu gansu sirruka da asrarai da magunguna da nayi posting shekaru da watanni da suka wuce a baya, abubuwa dayawa masu amfani suna nan a cikin shafina zaku samesu da izinin Allah, kuyi scrolling down ko top, Insha Allah 
Bayan haka ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
Tiktok: 
YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa


Ubangiji Allah yabamu ilimi mai amfani, Allah yasa mugama lafiya, Allah yabamu arziqi da lafiya wadatacciya
Next Post Previous Post
3 Comments
 • Unknown
  Unknown December 27, 2021 at 12:47 AM

  Enter your comment...masha allah allah ya biya malan

 • Anonymous
  Anonymous May 18, 2022 at 3:00 PM

  Masha Allahu muna Godiya

 • Anonymous
  Anonymous May 20, 2022 at 4:25 PM

  Masha Allah

Add Comment
comment url