Sirrin Cin Jarabawa Kowace Iri

SIRRIN CIN JARABAWA MAI WAHALA KO MAI SAUQI, KOKUMA KOWACE IRIN JARABAWA MA (Mujarrabun)

Assalamu alaikum wa rahmatullah ta'ala wa barakatuhu jama'a bayin Allah ƴan uwana ɗalibai da almajirai da yan makaranta da freshers da masu Interview da masu zuwa neman aiki da masu yin final year da masu yin screening da masu yin kowace irin jarabawa ma, yau wannan sirrin naku ne kyauta halak malak wannan bana wasa bane wallahi, wanda bazai iyaba yabada hanya, wannan aikin bana rago bane, bana unserious Students bane.

Jarabawa itace matakin ci gaban karatu na duk wani ɗalibi, itace makullin karatu, idan baka ci jarabawa ba bazaka ci gaba a karatunka ba, jarabawa itace komai a makaranta, ana samun matsala daga malamai da lecturers wasu daga cikin su suna yiwa ɗalibansu sharri da nuna musu qiyayya su kadasu, wasu kuma wahalar jarabawa ne kaje kayi karatu sosai amma kuma a tambayeka abunda ba shi ka karanta ba kokuma abunda baya cikin abunda aka baka ka karanta, kokuma tambayarda baka ganeba ko abunda baka ganeba, matsalolin sunada yawa, addu'a da jajircewa sune suke maganin komai sune maganin duk wata jarabawa mai wahala a ko ina ake yinta a ko ina take, Insha Allah ƴan uwana ɗalibai wannan sirrin naku ne ku aka yiwa shi musamman, ga aikin👇

Duk wanda kake so ka samu proceeding daga wurin sa ko wurin su, ko kake so ka ci jarabawa, to Insha Allah ko malaman suna so ko basa so ko masu Interview suna so ko basa so, duk wanda yake da alhakin sakamakon jarabawar ko yana so ko baya so dole yagan ka ya qyale ka, dole ne yayi haquri da iko da isar mulkin Allah wallahi, duk wanda zai iya daurewa yayi wannan sirrin to in dai zancen jarabawa ne to an wuceshi, saidai wata matsala daban.

Aikin yanada rikitarwa da wahala sosai, amma idan ka nutsu zaka gane aikin bashida wani wahala sosai 

Ba tareda ɓata lokaci ba ga yanda ake yin aikin 👇👇

NOTE: a samu/ a nemo jan ZAKARA mai kyau kafin a fara aikin.

Waɗanda suke neman cin jarabawa ta karatu ko ta tsallake wani mataki, ko interview ko terminal exam ko project da sauransu, to ga aikin da zaka yi kaci, kuma koda ace karatun ka yayi kyau ko baiyi ba, ko kayi karatu ko baka yiba sai kaci wallahi Insha Allah 

Da farko dai zaka je kasuwa wurin masu siyar da ganyen gargajiya kokuma maganin gargajiya kokuma masu siyar da itatuwan magani ka siyo FUREN FARAR BIYARANA Insha Allah za'a same shi a cikin irin waɗannan wuraren suna siyarwa, a tambaya sosai za'a dace, kuma ana siyar dashi bashi da tsada, in kasamu furen FUREN FARAR BIYARANA sai ka rubuta SURATUL YASEEN kokuma a rubuta maka SURATUL YASEEN qafa 7 amma za'a buɗe mimun mimun (minjayen) MUBEEN ɗin dukansu, ma'ana duk kowane MUBEEN za'a buɗe mimun ɗin, ga misalin yanda ake buɗe mimun ɗin 👇👇Suratul Yaseen tanada mubeen guda bakwai, saboda in sauqaqa muku al'amarin yanzu zan rubuto muku mubeen mubeen ɗin da Hausa dukansu, gasu kamar haka👇
 “Innã nahnu nuhyil mautã wanaktubu mã qaddamuu wa ããthãrahum, wa kulla shai'in ahsainããhu fee imãmin mubeen” 

“wamã alainãã illal balãgul mubeen”

“innee izan lafee dalãlin mubeen” 

“wa izã qeela lahum anfiquu mimmã razaqakumul lahu qalal lazeena kafaruu lillazeena ãmanu anuɗ'imu man lau yashã'ul lahu aɗ'amah in antum illa fee dalãlin mubeen“ 

“alam a'ahad ilaikum ya banee ãdama anla ta'abudush shaiɗãn innahu lakum aduwwun mubeen” 

“wamã allamnãhush shi'ira wamã yanbagee lah, in huwa illa zikrun wa qur'ãnun mubeen” 

“ awalam yaral insãnu annã khalaqnãhu min niɗfatin fa izã huwa khaseemun mubeen”

Waɗannan👆 sune mubeeen mubeen guda bakwai 7 na cikin suratul Yaseen

To a duk qafa ɗaya zaka samu mubin guda 7 kenan kamar yanda kuka gansu a sama, in an haɗa mubeen guda bakwai sau bakwai 7×7=49 jimla mubin 49 kenan, to su za'a rubuta

 A cikin mubeen mubeen ma'ana a cikin kowanne Mubeen ɗin zaka rubuta sunan makarantar da sunan malaman department ɗinku gabaɗaya, kokuma ka rubuta sunan aikin da sunan wadanda zasu yimuku interview din gabaɗaya, kokuma ka rubuta sunan project ɗin da sunan wadanda za'a yi depending project ɗin a hannunsu, za'a rubuta sunayen a cikin minjãyen (mimun mimun ɗin) bayan an rurrubuta sunayen sai a wanke rubutun sai a zuba wannan furen farar biyarana da ka siyo a ciki, sai ka sakasu a tukunya ka ɗorasu akan wuta kayita dafa su kana ba su wuta ruwan har su qare su shanye, bayan sun shanye kabar furaren susoyu su gasu a ciki har sai sun yi baqi qirin.

Note: akula akula: Amma fa a lokacinda ruwan suka qare saura furen sai kayita karanta surar (Yaseen) kafa 3 idan kazo mubeen sai ka ambaci sunayen malaman makarantar taku kokuma malaman department ɗin ku da duk wasu malamai masu ruwa da tsaki a abunda kake nema, haka zaka yita yi har ka gama kafa 3, a haka zakayi.

Bayan ka gama karanta Yaseen qafa uku ɗin sai ka sauke tukunyar daga kan wuta aikinka ya kammala ka gama Insha Allah, sai ka yanka jan zakaran naka wanda nace a tanadeshi tin a farkon aikin, wallahi idan har kaga baka ciba to ba'a yi jarabawar bane kawai malam, Insha Allah.

Wannan aikin GUARANTEE ne Mujarrabun ne

Sannan kuma bayan haka waɗanda suke da tambaya ko neman qarin bayani ko qarin haske kokuma masu shakku akan wani abu basu gane ba kokuma waɗanda na rubuta wani abu basu ganeba dakuma masu buqatar ayi musu wannan aikin su bayar da abun sadaqa sai su tuntuɓeni akan wannan numbar a WhatsApp ko sukirani 08136560680, ko 09020132884, in sun kira sun ji wayar tawa a kashe sai su tuntuɓeni da numbar a WhatsApp zasu sameni, waɗanda kuma suke da wata buqata ta daban zasu iya kira suyi bayani Insha Allah zamu yi qoqarin maganin wannan matsalar alfarmar annabi SAW

Sannan kuma bugu da ƙari akwai wasu magunguna daban daban kala kala a cikin wannan shafin nawa idan kun yi a qasa kokuma kun yi sama zaku kallesu, kuma kuyi saving din book mark da link na page ɗin nawa a browser ɗinku domin duba new update a page din

Sannan kuma waɗanda nayiwa alqawari zan kawo masu yanda ake yin Istihara ta asali ba jabu ba, amma kuma har yanzu ban kawo musu ba, hakan yaci tura, an samu matsala ne ban samu lokaci na gama haɗa bayanan istiharar ba shi yasa ban yi posting ba, dan Allah ina neman afuwa akan hakan.

Bayan haka ga link na WhatsApp group dinmu: https://chat.whatsapp.com/DfCzfdMbVNQ9adedPhDBLn
Tiktok: 
YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc akwai video yanda akeyin irin wannan ayyuka dayawa achan, kuyimana subscribing kuma kudanna qararrawa

Next Post Previous Post
2 Comments
  • Unknown
    Unknown October 28, 2021 at 3:29 AM

    Godiya Mukai

  • Anonymous
    Anonymous March 10, 2023 at 9:59 PM

    Toh Wanda besan sunan malaman bafa kamar Wanda zeje interview, screening test,da Kuma jarabawa Neman aiki ya zaiyi

Add Comment
comment url