Sirrin Biko/Sulhu Tsakanin Mata Da Miji

SULHUNTA TSAKANIN MATA DA MIJI, MATAR DA TAYI YAJI KOKUMA MIJIN DA YA QAURACEWA MATARSA 

Assalamu alaikum jama'a al'ummar Rasulullah SAW maza da mata yara da manya ɗalibai da malamai iyayen mu da kakannin mu qannen mu da yayyun mu, gwauraye da masu aure barkan ku da wannan lokaci da fatan kuna cikin yarda da amincin Allah maɗaukakin sarki da tsarewarsa amin, Allah yasa mugama da duniya lafiya Allah ya jiwan iyayen mu da magabatan mu ya gafarta musu amin.

Ina masu aure maza da mata kokuma in ce waɗanda suka yi yaji kokuma waɗanda matan su suka yi yaji, kokuma waɗanda suka samu matsala da mazajen su suka sake su kuma suka qi mayar da su, kokuma waɗanda suka saki matansu shiqa ɗaya ko biyu daga baya bayan sun huce sun je su mayar dasu amma abun ya ci tura, tace ba zata dawo ba kokuma mahaifiyarta ta ce ba zata koma ba ko babanta ya ce ba zata koma ba ko yayanta ya ce ba zata koma ba ko kawunta ya ce ba zata koma ba, kokuma ƴan gidansu ko yayunta mata sun daka qirji sun ce ba zata koma ba, kokuma ta haɗu da qawaye ƴan iska masu zuga sun zugata ta ce ba zata koma ba, kokuma tsohon saurayin ta ya hure mata kunne tace ba zata koma ba kokuma girman kan ta ya sa tace ba zata koka ba, kokuma dai wani dalili na banza yasa tace ba zata koma ba, kokuma ina wanda yake da uban gida ko ogan sa ko uban ɗakin sa ya koreshi ko sun yi faɗa ko an haɗasu faɗa ko an haɗa masa munafurci a gurin ogan nasa kokuma ana baqin ciki da kasancewar ku a tare shi yasa aka rabaka dashi aka sa ya koreka ba gaira ba dalili, to yau wannan sirrin naku ne.

Yau dai na qara dawowa kamar kullum da sirrin sulhu a tsakanin ma'auratan sunnah waɗanda suka samu saɓani kokuma wanda ya gujewa matarsa ya saketa yaqi zuwa bikonta yaqi neman ta, kokuma matar da tayi yaji ta tada fitina tabar gidan ka kokuma tayi qaura da bacin rai da fushi da rigima, kokuma kaine kake aiki a qarqashin wani sai kuka ɓata kokuma kuka samu matsala ko aka haɗa maka sharri a wurin sa, to ka kwantarda hankalinka ga yanda zaka yi ya dawo ko yana so ko baya so.

Aure sunnah ne sunnar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wa sallam, shi ne ya umarci dukkanin al'ummar musulmi da cewa su yi aure su hayayyafa domin yayi alfahari da mu a ranar tashin alqiyama, kuma ya ja hankalin mu gameda raunin mata da kuma zafin rai da illar shaiɗan da illar da yake yiwa al'umma musamman ma'aurata, zai dinga rura zuciyarsu ya hana su haquri ya dinga ziga mijin domin ya saki matarsa ko su samu matsala ya ci mutuncinta ta yanda zata bar gidan, kuma ya dinga zuga matar taqi yiwa mijin biyayya ta dinga yi masa rashin kunya da fitsara ko ta dinga gardama da shi ta daina yi masa abubuwan da hakki ne a kanta ta yi masa, saboda magance irin waɗannan matsalolin shi yasa muke bayar da irin waɗannan sirrukan, saboda Assulhu khair, sulhu alheri ne kuma gyara aure da zamantakewar aure lada ne dashi, kuma mutum yayi abunda Allah da annabi suke so, ba tareda ɓata lokaci sosai ba ga yanda aikin yake👇

Duk wanda ya samu matsala da matarsa ko kuma itace ta samu matsala da mijinta ko mutum ne da maigidansa suka ɓata kuma yana so su shirya amma baya so yaje gaban sa ya faɗa masa cewa haquri zai bashi kokuma yana so ya mayar dashi, kokuma matarka ce kana so ta dawo baka so kaje gidan su kokuma kabata haquri ko ka qasqantar da kan ka, to ga wannan aikin da zaka yi kamar haka:


A samu ko a nemo allo a rubuta wannan ayar Qafa bakwai (7) 👇


“Rabbanã innaka jãmi'un nãsi liyaumin lã raiba feehi innallãha lã yukhliful mee'ãd” qafa bakwai za'a rubuta da wannan hatimin shi kuma qafa ɗaya 1👇👇Bayan an rubuta ayar Qafa 7 da wannan hatimin qafa ɗaya (1) a tsakiyar hatimin inda aka rubuta "Ismun" da larabci, a nan za'a saka sunan wanda ake so a shirya dashi (mace ko namiji) a cikin hatimin a tsakiyar hatimin za'a rubuta sunan macene ko namiji ɗin, sai a naɗe layar aje wurin baduku ko masu ɗinka laya a kasuwa a ɗinkata ko a rufata, bayan an yi haka sai a rataya layar a jiki a dinga yawo da ita duk inda za'a je, to insha Allahu in dai tana jikinka to zata nemeka kokuma mai gidan naka zai neme ka dakan sa zai nemi ku sasanta wallahi insha allahu ta'alah alfarmar Sayyiduna Rasulillah SAW alhamdulilllah

Duk wanda yake neman qarin bayani to ya tuntuɓe ni a numbobina 08136560680, ko 09020132884 kokuma waɗanda suke neman wani sirri ko yi maka wani aiki daban za ku iya neman mu ta WhatsApp, kokuma zaku iya nemanmu ta email ku turamana saqo alameengobeer1@gmail.com
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url