Tarihin Shehudiezer

TARIHIN SHEHUDIEZER Assalamu alaikum warahmatullah ta'ala wa barakãtuh 

Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai, mai ikon yi da hanawa, ayau dai na yanke shawarar baku taqaitaccen tarihi na a gurguje.

Sunana Al-Ameen Abdulfattah, shekaruna 24, an haifeni a Katsina State amma ni ɗan Sokoto State ne asalina, inada ƴan uwana su goma sha biyar maza da mata, nafara karatun boko tin ina yaro iyayena suka sakani a Makaranta tareda ƴan uwana, nacigaba da karatu har Nagama Secondary School a Shekarar 2015, Nayi Jamb a Shekarar 2015 naci 226, nasamu Admission a Makarantar Usman Ɗanfodio University Sokoto, sukabani course maisuna Applied Chemistry, Saboda ana Strike na Malaman Jami'o'i (ASUU) da akeyi awannan shekarar hakan ne yasa banfara karatu achan ba, sai nashiga Sultan AbdulRahman School Of Health Technology Gwadabawa a shekarar 2016, nafara karatu nayi wata 6 a makarantar, daga nan naje Makarantar Karatun Alqur'ani da Ilimin Addinin Musulunci ta Darul Furqan Tsangaya Model School Damaturu, Yobe state aranar 22nd-April-2017, Nasamu nasarar yin karatuna har na hardace Qur'ani nayi satu narubuta Qur'ani dakaina a allo batareda kallon takarda ba, nabar Makarantar Darul Furqan 24th-May-2019, daga nan mahaifina ya samamun admission a makarantar Maryam Abacha American University of Niger, naje Jahar Maradi Jamhuriyar Nijar aranar 25th-May-2019 Nafara karatun Degree a Makarantar Maryam Abacha American University Of Niger, nagama Karatuna na Degree a 2nd- Nov-2022, ga al'ada result ɗin makarantarmu baya fitowa sai bayan wata 6 da kammala makaranta, nayi amfani da wannan damar wata 6 dana samu na rubuta Alqur'ani maigirma na baiwa Mahaifina, wannan kaɗan ne daga cikin rubutun Alqur'aninda nayi👇


Na fara rubuta wannan Qur'anin aranar 21st Nov-2022 nakammala rubutun Qur'anin da komai aranar laraba 23rd March 2022,, nakawowa mahaifina Qur'anin ranar juma'a 25th March 2022, na kasance ni kaɗai ne nayi karatun Qur'ani mai zurfi acikin gidanmu, bayan nan nakoma nayi karatun littattafai da ilimai na addinin musulunci harzuwa lokacinda Nakarbi certificate ɗina na Degree BSc in Computer Science (Second Class Upper) aranar 29-June-2022, kuma Alhamdulillah I've gained a lot of skills and experience during my academic career, Naje NYSC Orientation Camp aranar 22nd July 2022, munfito daga Camp 9th August 2022, nadawo gida 10th August, mahaifina Allah yayimasa rasuwa 19th August 2022 Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, my biggest lost, la haula wala quwwata illa billah, Allah yajiqansa yasakamasa da alkhairi, Allah yajiqan iyayenmu bakiɗaya, my dad👇


Nakarbi NYSC Certificate ɗina aranar 19th-July-2023, nafara rubuta Qur'ani na biyu ranar 23rd-July-2023 wanda haryanzu ina kan rubutashi saboda banason zaman banza, kuma Allah ya qaddara banida aikin yi, mahaifina shine gatana Allah ne gatana, tinda ya rasu rayuwa ta sauya, wanda inada yaqini inda yana raye da na samu aiki, amma alhamdulillah ala kullu hãl, ina neman addu'arku agareshi dakuma Addu'a Allah yabani aiki mai albarka wanda zai qaramun qwarin guiwa a kowane ɓangare na rayuwata kuma ya qaramun qaimi wurin taimakawa al'umma, domin shine kawai raunina ayanzu, Allah ya sakamuku da alkhairi, domin magana da shehudiezer ga numbobina 08136560680 (Call and WhatsApp) 09020132884 (Call)

Na zaɓi inbuɗe wannan website ne saboda ɓangare ne na karatunda nayi, kuma nabuɗe wannan hanyar ne domin in taimakawa al'umma a matsalolinsu na yau da kullum insamu lada mai gudana mara yankewa, kuma alhamdulilllah na taimaki dubban dubanin mutane, wasu ma daga qasashe daban daban kamar qasar Nijar, Cameroon, Chadi, Benin Republic, Cotonou, India, London, Italy, Gabon, etc. 

Wannan kaɗan daga cikin tarihina ne agurguje, Allah yabamu nasara a duniya da lahira, Allah yataimakemu yasa mudace, dani da ku da iyayena da iyayenku da ƴan uwana da ƴan uwanku da dukkanin mabiyana da followers da duk wanda ya karanta wannan posting ɗin nawa Allah ya haɗamu agidan aljannah Amin.

Follow me on Facebook: https://www.facebook.com/shehudiezer1

E-mail: alameengobeer1@gmail.com

Instagram: https://www.instagram.com/shehudiezer

Twitter: https://www.twitter.com/shehudiezer

Tiktok: https://www.tiktok.com/shehudiezer/

Threads: https://www.threads.net/@shehudiezer

YouTube Channel: https://youtube.com/@dandalinshehudiezer1819?si=FK_IusL29wplpNAc

AlhamdulillahNext Post Previous Post
1 Comments
  • Habiba Yusuf
    Habiba Yusuf October 2, 2023 at 3:05 PM

    Allah sarki malam, inama ace ni wata ce a Nigeria ko ni matar wani ce a Nigeria, da na nemamaka aiki yanda kake taimakonmu kaima Allah yataimakeka, mungode sosai muna yimaka fatan alkhairi dani da yan uwana

Add Comment
comment url